Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mika 4:9 - Littafi Mai Tsarki

9 Yanzu, me ya sa kike kuka da ƙarfi? Ba sarki a cikinki ne? Mashawarcinki ya hallaka ne, Da azaba ta auka miki kamar ta mace mai naƙuda?

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

9 Don me yanzu kike kuka da ƙarfi, ba ki da sarki ne? Masu shawararki sun hallaka ne, da zafi ya cika ki kamar mace mai naƙuda?

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mika 4:9
20 Iomraidhean Croise  

Dukansu za su firgita, azaba za ta ci ƙarfinsu kamar mace wadda take shan azabar naƙuda. Za su dubi juna a tsorace, fuskokinsu za su cika da kunya.


Abin da na gani, da abin da na ji a wahayin, ya razanar da ni, ya sa ni cikin azaba kamar ta mace mai naƙuda.


Kai ne, ya Ubangiji, ka sa muka yi kuka, Kamar macen da take naƙuda tana kuka da azaba.


Ya ku mazaunan Lebanon, Waɗanda suke zaune cikin itatuwan al'ul, Irin nishin da za ku yi sa'ad da azaba ta same ku, Azaba ce irin ta mace mai naƙuda!


Ubangiji ya ce, “Kada ka ji tsoro, ya barana Yakubu, Kada kuma ka yi fargaba, ya Isra'ila, Gama zan cece ka daga ƙasa mai nisa, Zan kuma ceci zuriyarka daga ƙasar bautarsu. Yakubu zai komo, ya yi zamansa rai a kwance, Ba kuwa za a tsoratar da shi ba.


Har yaushe zan yi ta ganin tuta, In yi ta jin amon ƙaho?


Na ji kuka kamar na mace wadda take naƙuda, Na ji nishi kamar na mace a lokacin haihuwarta ta fari, Na ji kukan 'yar Sihiyona tana kyakyari, Tana miƙa hannuwanta tana cewa, “Wayyo ni kaina, gama ina suma a gaban masu kisankai!”


Za a ci garuruwa da kagarai da yaƙi, A wannan rana zukatan sojojin Mowab Za su zama kamar zuciyar macen da take naƙuda.


Sarkin Babila ya ji labarinsu, Hannuwansa suka yi suwu. Wahala da azaba sun kama shi kamar mace mai naƙuda.


Ku ji kukan jama'ata ko'ina a ƙasar, “Ubangiji, ba shi a Sihiyona ne? Sarkinta ba ya a cikinta ne?” Ubangiji ya ce, “Me ya sa suka tsokane ni da sassaƙaƙƙun gumakansu, Da baƙin gumakansu?”


Shi wanda muke dogara gare shi, Wato zaɓaɓɓe na Ubangiji, ya auka cikin raminsu, Shi wanda muka ce, “A ƙarƙashin inuwarsa ne za mu zauna a cikin sauran al'umma.”


Gama yanzu za su ce, “Ba mu da sarki, Domin ba mu ji tsoron Ubangiji ba. Amma me sarki zai yi mana?”


Naƙudar haihuwarsa ta zo, Amma shi wawan yaro ne, Bai fito daga mahaifar ba.


Gama mutanen Isra'ila za su zauna kwanaki da yawa ba sarki, ba shugaba, ba sadaka, ba al'amudi, ba falmaran, ba kan gida.


Domin haka zai yashe su, Sai lokacin da wadda take naƙuda ta haihu. Sa'an nan sauran 'yan'uwansa Za su komo wurin mutanen Isra'ila.


Idan mace tana naƙuda takan sha wuya, don lokacin haihuwarta ya yi. Amma da zarar ta haifi jinjirin, ba ta ƙara tunawa da wahalar da ta sha, domin murnar an sami baƙon duniya.


Tana da ciki, sai kuma ta yi ta ƙara ta ƙagauta domin ta haihu, saboda azabar naƙuda.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan