Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mika 4:8 - Littafi Mai Tsarki

8 “Ke kuma hasumiyar garken tumaki, tudun Sihiyona, Mulki na dā zai komo wurinki, Wato sarautar Urushalima.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

8 Game da ke, ya hasumiyar tsaron garke, Ya mafaka Diyar Sihiyona, za a maido miki da mulkinki na dā, sarauta kuma za tă zo wa Diyar Urushalima.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mika 4:8
23 Iomraidhean Croise  

Isra'ila ya ci gaba da tafiyarsa, ya kuwa kafa alfarwarsa daura da hasumiyar Eder.


Duk da haka Dawuda ya ci kagarar Sihiyona, wato birnin Dawuda.


Falal ɗan Uzai, ya gyara wani sashi daga kusurwar da hasumiyar benen gidan sarki a wajen shirayin matsara. Bayansa kuma sai Fedaiya ɗan Farosh ya yi gyare-gyare.


A buɗe ƙofofi sosai, A buɗe daɗaɗɗun ƙofofi, Babban Sarki kuwa zai shigo!


Allah ya nuna akwai zaman lafiya a wurinsa, A kagarar birnin.


Kai ne kāriyata mai ƙarfi Da take kiyaye ni daga maƙiyana.


Wuyanki kamar hasumiyar Dawuda yake, kewayayye sumul sumul, Inda aka rataye garkuwoyi dubu na jarumawa.


Zan ba ku shugabanni da mashawarta kamar waɗanda kuke da su dā can. Sa'an nan za a ce da Urushalima adala, amintaccen birni.”


Yau abokan gāba suna cikin Nob, daga can suke nuna wa Dutsen Sihiyona yatsa, wato wanda yake cikin Urushalima.


Ya kauce ƙasar ya tsintsince duwatsun, Ya daddasa itatuwan inabi mafi kyau. Ya gina hasumiya don a yi tsaronsu, Ya kuma haƙa rami inda za a matse 'ya'yan inabin. Ya yi ta jira don 'ya'yan inabin su nuna, Amma ko wannensu tsami take gare shi.


A kwanakin waɗannan sarakuna, Allah na Sama zai kafa wani mulki wanda ba zai taɓa rushewa ba har abada, ba kuma za a gādar da shi ga waɗansu mutane ba. Wannan mulki zai ragargaje dukan waɗannan mulkoki, ya kawo ƙarshensu. Wannan mulki zai dawwama har abada.


Amma tsarkaka na Maɗaukaki za su karɓi mulki, su kuwa riƙe mulkin har abada abadin.


Isra'ilawa za su hau Dutsen Sihiyona, su cece shi, Za su mallaki dutsen Isuwa, Ubangiji ne Sarki.


“Hakika zan tattara ku duka, ya Yakubu, Zan tattara ringin Isra'ila. Zan haɗa su tare kamar tumaki a garke, Kamar garken tumaki a makiyaya Za su zama taron jama'a mai hayaniya.


Ubangiji ya ce, “Zan datse karusa daga Ifraimu, In datse ingarman yaƙi a Urushalima, Zan kuma karya bakan yaƙi. Sarkinki zai tabbatar wa al'umman duniya da salama, Mulkinsa zai zama daga teku zuwa teku, Daga Kogin Yufiretis zuwa matuƙar duniya.”


Ku koma mafakarku, ku ɗaurarru masu sa zuciya. Gama yanzu zan sāka muku har ninki biyu.


Ki yi murna ƙwarai, ya Sihiyona! Ta da murya ya Urushalima! Ga Sarkinki yana zuwa wurinki, Shi mai adalci ne, mai nasara, Shi kuma mai tawali'u ne, Yana bisa kan jaki, a kan aholaki.


Yakubu zai yi mulki, Zai hallaka waɗanda suka ragu cikin birni.”


“To, ga kuma wani misali. An yi wani maigida da ya yi garkar inabi, ya shinge ta, ya haƙa ramin matse inabi a ciki, ya kuma gina wata 'yar hasumiyar tsaro. Ya ba waɗansu manoma sufurin garkar, sa'an nan ya tafi wata ƙasa.


Sai Yesu ya fara yi musu magana da misalai ya ce, “Wani mutum ne ya yi garkar inabi, ya shinge ta, ya haƙa ramin matse inabin, ya kuma gina wata 'yar hasumiyar tsaro. Ya ba waɗansu manoma sufurin garkar, sa'an nan ya tafi wata ƙasa.


a can a birbishin dukkan sarauta da iko, da ƙarfi, da mulki, a birbishin kowane suna da za a sa, ba ma a duniyar nan kawai ba, har ma a lahira ma.


Ba za a ƙara yin dare ba, ba za su bukaci hasken fitila, ko na rana ba, domin Ubangiji Allah zai haskaka su, za su kuma sha ni'imar Mulki har abada abadin.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan