Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mika 4:6 - Littafi Mai Tsarki

6 Ubangiji ya ce, “A waccan rana zan tattara guragu, Da waɗanda aka kora, Da waɗanda na wahalshe su.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

6 “A wannan rana,” in ji Ubangiji, “zan tattara guragu; zan kuma tara masu zaman bauta, da waɗanda na sa suka damu.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mika 4:6
16 Iomraidhean Croise  

Ubangiji yana rayar da Urushalima, Yana komo da waɗanda aka kai su baƙunci a wata ƙasa.


Ina gab da fāɗuwa, Ina cikin azaba kullum.


Haka Ubangiji Allah, shi wanda ya tattara Isra'ilawa korarru, ya faɗa, ya ce, “Zan ƙara tattaro waɗansu, bayan waɗanda na riga na tattara.”


A waɗannan kwanaki mutanen Yahuza za su haɗu da mutanen Isra'ila. Tare za su zo daga ƙasar arewa zuwa cikin ƙasar da na ba kakanninku gādo.”


Ga shi, zan fito da su daga ƙasar arewa, Zan tattaro su daga manisantan wurare na duniya, Tare da su makafi da guragu, Da mace mai goyo da mai naƙuda, Za su komo nan a babbar ƙungiya.


Zan kwaso ku daga cikin al'ummai, in tattaro ku daga dukan ƙasashe, in kawo ku cikin ƙasarku.


“Hakika zan tattara ku duka, ya Yakubu, Zan tattara ringin Isra'ila. Zan haɗa su tare kamar tumaki a garke, Kamar garken tumaki a makiyaya Za su zama taron jama'a mai hayaniya.


Ga shi kuwa, a wannan lokaci Zan hukunta masu zaluntarki, Zan kuma ceci gurgu, Zan tattara korarru, Zan mai da kunyarsu ta zama yabo, Za su yi suna a duniya duka.


Don Ɗan Mutum ya zo ne musamman garin neman abin da ya ɓata, yă cece shi kuma.”


Ina kuma da waɗansu tumaki da ba na wannan garke ba ne. Su ma lalle in kawo su, za su kuwa saurari muryata, su zama garke guda, makiyayi kuma guda.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan