Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mika 4:4 - Littafi Mai Tsarki

4 Kowa zai zauna gindin kurangar inabinsa da gindin ɓaurensa. Ba wanda zai tsoratar da shi, Gama Ubangiji Mai Runduna ne ya faɗa.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

4 Kowa zai zauna a tushen kuringar inabinsa da tushen ɓaurensa, kuma ba wanda zai tsoratar da su, gama Ubangiji Maɗaukaki ne ya faɗa.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mika 4:4
25 Iomraidhean Croise  

Mutanen Yahuza da na Isra'ila suka zauna lafiya tun daga Dan har Biyersheba. Kowa ya yi zamansa a gida dukan kwanakin Sulemanu.


Ubangiji kuma ya yi wa tsohona Dawuda alkawari ya ce, ‘Ɗanka, wanda zai gāje ka, shi zai gina mini Haikali.’ Yanzu kuwa na yi niyyar gina wannan haikali domin sujada ga Ubangiji Allahna.


Ba za ka ji tsoron kowane maƙiyi ba, Mutane da yawa za su nemi taimako daga gare ka.


Ka sa ƙasar ta mori wadatarta, Ka sa al'ummar ta san adalci.


Ba za ka damu da masifar da za ta auko farat ɗaya ba, irin wadda takan auka wa mugaye kamar hadiri.


Amma idan kuka ƙi, kuka raina ni, mutuwa ce ƙaddararku. Ni Ubangiji na faɗi wannan.”


Za a watse a bar biranen Suriya har abada. Za su zama makiyayar tumaki da shanu. Ba wanda zai tsoratar da su.


Sa'ad da wannan ya faru ragayar da aka ɗaura tam za ta tsinke ta fāɗo. Wannan shi ne ƙarshen kowane abin da aka sa a cikin ragayar ke nan. Ni Ubangiji Mai Runduna na faɗa.”


Ka hukunta jama'arka, ya Ubangiji, A cikin azaba sun yi addu'a gare ka.


Gama kowa zai yi abin da yake daidai, za a sami salama da zaman lafiya har abada.


Kada ku kasa kunne ga Hezekiya. Sarkin Assuriya yana umartarku ku fito daga cikin birni ku sallama. Za a yardar muku duka ku ci 'ya'yan inabi daga gonakinku, da 'ya'yan ɓaure na itatuwan ɓaurenku, ku kuma sha ruwa daga rijiyoyinku na kanku,


Sa'an nan za a bayyana ɗaukakar Ubangiji, Dukan 'yan adam kuwa za su gan ta. Ubangiji ne kansa ya yi wannan alkawari.”


Adalci da gaskiya za su ƙarfafa ki. Za ki tsira daga shan zalunci da razana. Gama ba za su kusace ki ba.


sa'an nan ne za ku yi murna cikin Ubangiji, zan sa ku a kan maɗaukakan wurare na duniya. Zan kuma ciyar da ku da gādon mahaifinku Yakubu, ni Ubangiji na faɗa.”


Zan sa makiyayan da za su lura da su. Ba kuwa za su ƙara jin tsoro, ko razana ba, ba kuma wanda zai ɓace, ni Ubangiji na faɗa.


Ubangiji ya ce, “Kada ka ji tsoro, ya barana Yakubu, Kada kuma ka yi fargaba, ya Isra'ila, Gama zan cece ka daga ƙasa mai nisa, Zan kuma ceci zuriyarka daga ƙasar bautarsu. Yakubu zai komo, ya yi zamansa rai a kwance, Ba kuwa za a tsoratar da shi ba.


“Zan yi alkawarin salama da su. Zan kuwa kori namomin jeji daga ƙasar, domin tumakin su zauna lafiya a jeji, su kwana cikin kurmi.


Ba za su ƙara zama ganimar al'ummai ba, namomin jejin ƙasar kuma ba za su cinye su ba. Za su yi zamansu lafiya, ba wanda zai tsorata su.


ka ce, ‘Zan haura, in tafi ƙasar da garuruwanta ba su da garu, in fāɗa wa mutanen da suke zama cikin salama, dukansu kuwa suna zaman lafiya, garuruwansu ba garu, ba su da ko ƙyamare,


Sa'ad da suka komo suka zauna lafiya a ƙasarsu, za su manta da abin kunyar da suka yi da dukan ha'incin da suka yi mini. Ba wanda zai ƙara firgita su, ba kuwa mai tsorata su.


“Zan ba da salama cikin ƙasar. Za ku kwanta, ba abin da zai razana ku. Zan kawar da mugayen dabbobi daga ƙasar. Ba za a ƙara yin yaƙi a ƙasarku ba.


Domin haka zai yashe su, Sai lokacin da wadda take naƙuda ta haihu. Sa'an nan sauran 'yan'uwansa Za su komo wurin mutanen Isra'ila.


Waɗanda suka ragu cikin Isra'ila, Ba za su aikata mugunta ba, Ba kuma za su faɗi ƙarya ba, Gama harshen ƙarya ba zai kasance a bakinsu ba. Za su yi kiwo, su kwanta, Ba wanda zai tsorata su.”


A wannan rana kowane ɗayanku zai gayyaci maƙwabcinsa zuwa gindin kurangar inabinsa da itacen ɓaurensa.’ ”


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan