Mika 4:3 - Littafi Mai Tsarki3 Zai shara'anta tsakanin al'umman duniya masu yawa, Zai sulhunta jayayyar da take tsakanin manyan al'ummai, Za su mai da takubansu garemani, Māsunsu kuma su maishe su wuƙaƙen aske itace. Al'umma ba za ta ƙara fita zuwa yaƙi ba, Ba za su ƙara koyon yaƙi ba. Faic an caibideilSabon Rai Don Kowa 20203 Zai shari’anta tsakanin mutane yă kuma sulhunta tsakanin manyan al’ummai nesa da kuma kusa. Har su mai da takubansu su zama garemani, māsunsu kuma su zama wuƙaƙen askin itace. Al’umma ba za tă ɗauki takobi gāba da wata al’umma ba, ko a yi horarwa don yaƙi. Faic an caibideil |