Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mika 4:2 - Littafi Mai Tsarki

2 Al'umman duniya za su zo, su ce, “Bari mu haura zuwa tudun Ubangiji, Zuwa Haikalin Allah na Isra'ila, Za mu koyi abin da yake so mu yi, Za mu yi tafiya a hanyar da ya zaɓa.” Koyarwar Ubangiji daga Urushalima take zuwa, Daga Sihiyona yake magana da jama'arsa.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

2 Al’ummai da yawa za su zo su ce, “Ku zo, bari mu haura zuwa dutsen Ubangiji, zuwa gidan Allah na Yaƙub. Zai koya mana hanyoyinsa, don mu yi tafiya cikin hanyoyinsa.” Doka za tă fita daga Sihiyona, maganar Ubangiji kuma daga Urushalima.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mika 4:2
35 Iomraidhean Croise  

Tun daga Sihiyona Ubangiji zai faɗaɗa sarautarka, ya ce, “Ka yi mulki bisa maƙiyanka.”


Masu farin ciki ne, marasa laifi cikin zamansu, Waɗanda suke zamansu bisa ga dokar Ubangiji.


Zan yabe ka kullayaumin Domin ka koya mini ka'idodinka.


Na yi murna sa'ad da suka ce mini, “Tashi mu tafi Haikalin Ubangiji!”


Waɗanda suke biyayya da Ubangiji Za su koyi hanyar da za su bi daga gare shi.


Jama'arsu za su ce, “Bari mu haura zuwa tudun Ubangiji, Zuwa ga Haikalin Allah na Isra'ila. Za mu koyi abin da yake so mu yi, Za mu yi tafiya a hanyar da ya zaɓa. Koyarwar Ubangiji daga Urushalima take zuwa, Daga Sihiyona yake magana da jama'arsa.”


“Ni kaina zan koya wa mutanenki, Zan kuwa ba su wadata da salama.


“Zan kai ku tsattsarkan dutsena, in sa ku yi murna a masujadata. Hadayunku na ƙonawa da sadakokinku za su zama abin karɓa a bagadena. Za a kira Haikalina wurin yin addu'a na dukan jama'a.”


Gama rana tana zuwa sa'ad da mai tsaro zai yi kira A ƙasar tudu ta Ifraimu, ya ce, ‘Ku tashi mu haura zuwa Sihiyona Zuwa wurin Ubangiji Allahnmu.’ ”


Ka yi mana addu'a domin Ubangiji Allahnka ya nuna mana hanyar da za mu bi, da kuma abin da za mu yi.”


Mu nace domin mu san Ubangiji Zuwansa tabbatacce ne kamar wayewar gari. Zai zo wurinmu kamar ruwan sama, Kamar ruwan bazara da yake shayar da ƙasa.”


Sa'an nan wanda ya ragu daga cikin dukan al'umman da suka kai wa Urushalima yaƙi zai riƙa haurawa zuwa Urushalima kowace shekara, domin yi wa Ubangiji Maɗaukakin Sarkin sujada a lokacin kiyaye Idin Bukkoki.


“A wannan rana al'umman duniya da yawa za su haɗa kai da Ubangiji, za su kuwa zama jama'ata, ni kuma zan zauna a tsakiyarki. Za ki sani Ubangiji Mai Runduna ya aike ni gare ki.


Ubangiji ya ce, “Zan datse karusa daga Ifraimu, In datse ingarman yaƙi a Urushalima, Zan kuma karya bakan yaƙi. Sarkinki zai tabbatar wa al'umman duniya da salama, Mulkinsa zai zama daga teku zuwa teku, Daga Kogin Yufiretis zuwa matuƙar duniya.”


Su kuwa suka tafi, suka yi ta wa'azi ko'ina, Ubangiji yana taimakonsu, yana kuma tabbatar da maganarsu ta mu'ujizan nan da suke biye da maganar.]


a kuma yi wa dukan al'ummai wa'azi su tuba, a gafarta musu zunubansu saboda sunansa. Za a kuwa fara daga Urushalima.


A rubuce yake cikin littattafan annabawa cewa, ‘Dukkansu Allah ne zai koya musu.’ To, duk wanda ya ji, ya kuma koya wurin Uba, zai zo gare ni.


Duk mai son aikata nufin Allah zai san koyarwan nan ko ta Allah ce, ko domin kaina nake faɗa.


Amma za ku sami iko sa'ad da Ruhu Mai Tsarki ya sauko muku, za ku kuma zama shaiduna a Urushalima, da duk ƙasar Yahudiya, da ta Samariya, har ya zuwa iyakar duniya.”


Suna fita majami'a ke nan, sai mutane suka roƙe su su ƙara yi musu wannan magana a ran Asabar mai zuwa.


ta wurin ikon mu'ujizai, da abubuwan al'ajabai, da kuma ta wurin ikon Ruhun, har dai daga Urushalima da kewayenta, har zuwa Ilirikun, na yi bisharar Almasihu a ko'ina.


“Waɗannan su ne umarnai, da dokoki, da farillai waɗanda Ubangiji Allahnku ya umarce ni in koya muku domin ku kiyaye su a ƙasar da kuke hayewa zuwa ciki don ku mallake ta,


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan