Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mika 3:3 - Littafi Mai Tsarki

3 Kuna cin naman mutanena, kuna feɗe fatar jikinsu, Kuna kakkarya ƙasusuwansu, Kuna yanyanka su gunduwa gunduwa kamar naman da za a sa a tukunya.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

3 ku da kuke cin naman mutanena, ku feɗe fatar jikinsu kuke kakkarya ƙasusuwansu, kuke yayyanka su gunduwa-gunduwa kamar naman da za a toya, kamar naman da za a sa a dafa.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mika 3:3
11 Iomraidhean Croise  

Ubangiji ya ce, “Ba su sani ba? Duk waɗannan masu aikin mugunta jahilai ne? Ta wurin yi wa jama'ata fashi suke zaman gari, Ba su yin addu'a gare ni.”


Sa'ad da mugaye suka tasar mini, Suna ƙoƙari su kashe ni, Za su yi tuntuɓe su fāɗi.


Akwai waɗansu mutane waɗanda haƙoransu takuba ne, mataunansu kuma wuƙaƙe ne, don su cinye matalauta da masu fatara daga duniya.


Ubangiji ya kawo dattawa da shugabannin jama'arsa a gaban shari'a. Ga laifin da ya same su da shi, “Kun washe gonakin inabi, kun cika gidajenku da abin da kuka ƙwato daga matalauta.


Ba ku da izinin da za ku ragargaza jama'ata, ku cuci matalauta, ni Ubangiji Mai Runduna na faɗa.”


Waɗanda suke cewa, ‘Lokacin gina gidaje bai yi kusa ba. Wannan birni tukunya ce mai ɓararraka, mu ne kuwa naman.’


Ka zuba gunduwoyin nama a ciki, Dukan gunduwoyi masu kyau, wato cinya da kafaɗa, Ka cika ta da tantakwashi.


Ku ji wannan, ku da kuke tattake masu bukata, kuna ƙoƙari ku hallakar da matalautan ƙasar.


Ubangiji ya amsa ya ce, “Ba da daɗewa ba mutanena sun tashi kamar maƙiyi, Kukan tuɓe rigar masu wucewa da salama, masu komawa da yaƙi.


Shugabanninsa zakoki ne masu ruri, Alƙalansa kuma kyarketai ne da sukan fito da maraice, Waɗanda ba su rage kome kafin wayewar gari.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan