Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mika 2:3 - Littafi Mai Tsarki

3 Domin haka Ubangiji ya ce, Ga shi, yana shirya wa wannan jama'a masifa, Wadda ba za ku iya kuɓuta daga cikinta ba. Ba kuma za ku yi tafiyar alfarma ba, Gama mugun lokaci ne.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

3 Saboda haka, Ubangiji ya ce, “Ina shirya wa waɗannan mutane bala’i, yadda ba za ku iya ceton kanku ba. Ba za ku ƙara tafiya kuna taƙama ba, gama zai zama lokacin bala’i ne.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mika 2:3
29 Iomraidhean Croise  

Zai zama ƙarshen waɗanda suke zaluntar waɗansu, suna raina Allah. Za a hallakar da kowane mai zunubi.


Ubangiji ya ce, “Duba irin girmankai da matan Urushalima suke da shi! Suna tafe suna hura hanci, a koyaushe suna ta fara'a irin ta yaudara, suna takawa ɗaya ɗaya a hankali da mundaye a ƙafafunsu, suna cas cas.


Kukan ce, “Bari Ubangiji ya gaggauta ya aikata abin da ya ce zai yi don mu gani. Bari Allah, Mai Tsarki na Isra'ila, ya i da shirye-shiryensa. Bari mu ga abin da yake nufi.”


Saboda haka yanzu, sai ka faɗa wa jama'ar Yahuza da mazaunan Urushalima, ka ce, haka Ubangiji ya faɗa, ‘Ga shi, na shirya muku masifa, ina tsara wahalar da za ta same ku. Bari kowannenku ya koma ya bar muguwar hanyarsa, ya gyara al'amuransa da ayyukansa.’


Sai na faɗa wa Zadakiya Sarkin Yahuza wannan magana cewa, “Ka ɗaura karkiyar Sarkin Babila a wuyanka, ka bauta masa, shi da mutanensa, don ka rayu!


Domin haka ni Ubangiji na ce, ba biyayya kuka yi mini ba, da irin shelar 'yancin da kowannenku ya yi wa ɗan'uwansa da maƙwabcinsa, saboda haka ni zan yi muku shelar 'yanci zuwa mutuwa ta takobi, da annoba, da yunwa. Zan sa ku zama abin ƙyama ga dukan mulkokin duniya.


Da Yehudi ya karanta sakin layi uku ko huɗu sai sarki ya sa wuƙa ya yanke su, ya zuba a wutar da take ci a kasko, da haka ya ƙone littafin duka.


sai Yazaniya ɗan Hoshaiya, da Yohenan ɗan Kareya, da dukan 'yan tsagera, suka ce wa Irmiya, “Ƙarya kake yi, Ubangiji Allahnmu bai aiko ka da cewa kada mu tafi, mu zauna a Masar ba!


Sauran mutanen muguwar tsaran nan waɗanda suke a wuraren da na warwatsa su, za su fi son mutuwa fiye da rayuwa. Ni Ubangiji Mai Runduna na faɗa.”


“Ubangiji ya tattara laifofina Ya yi karkiya da su, Ya ɗaura su a wuyana, Ya sa ƙarfina ya kāsa. Ya kuma bashe ni a hannun Waɗanda ban iya kome da su ba.


Ubangiji ya aikata abin da ya yi niyya, Ya cika maganarsa wadda ya faɗa tun dā, Ya hallakar, ba tausayi, Ya sa maƙiyi ya yi murna a kanki, Ya ƙarfafa ƙarfin maƙiyanki.


Masu binmu a ƙyeyarmu suke, suna korarmu da zafi, Mun gaji, ba a yarda mu huta.


Yanzu ni, Nebukadnezzar, ina yabon Sarkin Samaniya, ina ɗaukaka shi, ina kuma girmama shi saboda dukan ayyukansa daidai ne, al'amuransa kuma gaskiya ne. Yakan ƙasƙantar da masu girmankai.”


Ko masu saurin gudu ma ba za su tsere ba, Ƙarfafa za su zama kumamai, Sojoji kuma ba za su iya ceton kansu ba.


Jama'ar Isra'ila, ku kasa kunne ga wannan saƙo da Ubangiji ya aiko muku, ya ce, “Na fitar da iyalanku duka daga Masar.


“Daga cikin dukan al'umman da nake ƙauna a duniya, Ku kaɗai ne na sani, Nake kuma kulawa da ku, Don haka zan hukunta ku saboda zunubanku.”


Ashe, ba abin mamaki ba ne, Da masu hankali suka kame bakinsu A waɗannan kwanaki na mugunta.


Taku ta ƙare, ku masu shirya mugunta, Masu tsara mugunta a gadajensu! Sa'ad da gari ya waye, sai su aikata ta, Domin ikon aikatawa yana hannunsu.


waɗanda suka kasai da ransu saboda ni, ba kuwa ni kaɗai nake gode musu ba, har ma da dukkan ikilisiyoyin al'ummai.


Ku yi matuƙar amfani da lokaci don kwanaki mugaye ne.


domin haka za ku bauta wa magabtanku waɗanda Ubangiji zai turo muku. Za ku bauta musu da yunwa, da ƙishirwa, da tsiraici, da talauci. Za su sa karkiyar ƙarfe a wuyanka har su hallaka ku.


Gama Shari'a marar jinƙai ce ga wanda ba ya nuna jinƙai. Amma jinƙai yana rinjayar hukunci.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan