Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mika 1:3 - Littafi Mai Tsarki

3 Ga shi, Ubangiji yana fitowa daga wurin zamansa, Zai sauko, ya taka kan tsawawan duwatsun duniya.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

3 Duba! Ubangiji yana zuwa daga wurin zamansa; zai sauko yă taka maɗaukakan wuraren duniya.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mika 1:3
15 Iomraidhean Croise  

Ka dubi dukan wanda yake alfarma ka ƙasƙantar da shi, Ka tattake mugaye a inda suke.


Allahnmu yana Sama, Yana aikata yadda yake so.


Ubangiji zai kiyaye Dutsen Sihiyona, amma za a tattake jama'ar Mowab a ƙasa, kamar yadda ake tattake tattaka cikin taki.


Ubangiji yana zuwa ya hukunta jama'arsa a duniya saboda zunubansu. Kashe-kashen da aka yi a duniya a ɓoye, za a bayyana su, ƙasa ba za ta ƙara ɓoye waɗanda aka kashe ba.


Sa'an nan Ruhu ya ɗaga ni, sai na ji murya a bayana, kamar babban motsi, tana cewa, “Yabo ga ɗaukakar Ubangiji a kursiyinsa.”


Allah ne ya yi duwatsu Ya kuma halicci iska. Ya sanar da nufinsa ga mutum, Ya juya rana ta zama dare. Yana sarautar duniya duka. Sunansa kuwa Ubangiji Maɗaukaki!


Ubangiji Allah Mai Runduna Ya taɓi duniya, ta girgiza. Duk waɗanda suke zaune cikinta Suna baƙin ciki. Duniya duka takan hau Ta kuma gangara kamar ruwan Kogin Nilu.


Ubangiji Allah shi ne ƙarfina, Ya sa ƙafafuna su zama kamar na bareyi, Ya kuma sa ni in yi tafiya a cikin maɗaukakan wurare.


A wannan rana ƙafafunsa za su tsaya a bisa Dutsen Zaitun wanda yake wajen gabas da Urushalima. Dutsen Zaitun zai tsage biyu daga gabas zuwa yamma, ya zama babban kwari. Sashi guda na dutsen zai janye zuwa wajen kudu. Ɗaya sashin kuma zai janye zuwa wajen arewa.


“Ya sa shi ya hau kan tuddai, Ya ci amfanin ƙasa, Ya sa shi ya sha zuma daga dutse, Ya ba shi mai daga dutsen ƙanƙara.


Mai farin ciki ne kai, ya Isra'ila! Wane ne kamarku, mutanen da Ubangiji ya ceta? Ubangiji ne garkuwarku, Shi ne kuma takobinku mai daraja. Magabtanku za su yi muku fādanci, Amma ku za ku tattake masujadansu.”


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan