Mika 1:2 - Littafi Mai Tsarki2 Dukanku ku ji, ku al'ummai! Ki kasa kunne, ya duniya, da dukan abin da yake cikinki. Bari Ubangiji Allah Daga Haikalinsa mai tsarki ya zama shaida a kanku. Faic an caibideilSabon Rai Don Kowa 20202 Ku ji, ya ku mutane duka, ki saurara, ya ke duniya da dukan mazauna cikinki, bari Ubangiji Mai Iko Duka yă zama shaida a kanku, daga haikalinsa mai tsarki. Faic an caibideil |
Ubangiji Mai Runduna ya ce, “Zan zo wurinku domin in yi shari'a. Nan da nan zan tabbatar da laifin masu yin sihiri, da na mazinata, da na masu shaidar zur, da na masu zaluntar ma'aikata a kan albashinsu, da waɗanda suke ƙwarar gwauraye, wato matan da mazansu suka mutu, da marayu, da baƙi, da waɗanda ba su ganin girmana.”