Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mika 1:1 - Littafi Mai Tsarki

1 Ubangiji ya yi magana da Mika mutumin Moreshet a zamanin Yotam, da na Ahaz, da na Hezekiya, sarakunan Yahuza. Ya yi masa magana a kan Samariya da Urushalima.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

1 Maganar Ubangiji ta zo wa Mika mutumin Moreshet a zamanin Yotam, da na Ahaz, da kuma na Hezekiya, sarakunan Yahuda, Mika ya ga wahayi a kan Samariya da kuma a kan Urushalima. Ga abin da ya ce.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mika 1:1
27 Iomraidhean Croise  

A shekara ta biyu ta sarautar Feka ɗan Remaliya Sarkin Isra'ila, Yotam ɗan Azariya Sarkin Yahuza, ya ci sarauta.


Sai Ubangiji ya buge shi da kuturta, ya kuwa zama kuturu har ran da ya rasu. Ya zauna a wani gida a ware. Sai Yotam ɗansa ya zama wakilin gidan, yana kuma mulkin jama'ar ƙasar.


A shekara ta goma sha bakwai ta sarautar Feka ɗan Remaliya, Ahaz ɗan Yotam Sarkin Yahuza, ya ci sarauta.


A shekara ta uku ta sarautar Hosheya ɗan Ila Sarkin Isra'ila, Hezekiya ɗan Ahaz Sarkin Yahuza ya ci sarautar.


Ahaz yana da shekara ashirin sa'ad da ya ci sarauta, ya yi shekara goma sha shida yana mulki a Urushalima. Amma shi bai yi abin da yake daidai a gaban Ubangiji kamar yadda kakansa Dawuda ya yi ba.


Hezekiya ya ci sarauta sa'ad da yake da shekara ashirin da biyar. Ya yi mulki shekara ashirin da tara a Urushalima. Sunan tsohuwarsa Abaija, 'yar Zakariya.


Abin da yake rubuce a littafin nan, jawabi ne a kan Yahuza da Urushalima, wanda Allah ya bayyana wa Ishaya ɗan Amoz a zamanin da Azariya, da Yotam, da Ahaz, da Hezekiya, suka yi sarautar Yahuza.


Ubangiji ya ce, “Duniya da sararin sama, ku kasa kunne ga abin da ni, Ubangiji, nake cewa! 'Ya'yan da na goya sun tayar mini.


Sa'ad da sarki Ahaz, ɗan Yotam, wato jikan Azariya yake mulkin Yahuza, sai yaƙi ya ɓarke. Rezin, Sarkin Suriya, da Feka ɗan Remaliya, Sarkin Isra'ila, suka fāɗa wa Urushalima da yaƙi, amma ba su iya cinta ba.


Samariya ita ce ƙarfin Isra'ila, sarki Feka kuma shi ne ƙarfin Samariya. “Idan bangaskiyarku ba ta da ƙarfi, to, ba za ku dawwama ba.”


“Mika kuwa, mutumin Moreshet, ya yi annabci a kwanakin Hezekiya, Sarkin Yahuza, ya faɗa wa dukan mutanen Yahuza cewa, “ ‘Ga abin da Ubangiji Mai Runduna ya ce, Za a nome Sihiyona kamar gona, Urushalima kuwa za ta zama tsibin juji, Ƙwanƙolin dutsen Haikalin zai zama kurmi.’


Ubangiji kuwa ya yi magana da Yusha'u ɗan Beyeri a zamanin mulkin Azariya, da Yotam, da Ahaz, da Hezekiya, sarakunan Yahuza, da zamanin mulkin Yerobowam ɗan Yehowash, Sarkin Isra'ila.


“Ko da yake mutanen Isra'ila suna karuwanci, Kada kuma mutanen Yahuza su yi laifi. Kada ku tafi Gilgal, Ko ku haura zuwa Bet-awen. Kada ku yi rantsuwa da cewa, ‘Har da zatin Ubangiji!’


“Gama mutanen Isra'ila sun manta da Mahaliccinsu, Sai sun gina manyan gidaje masu daraja. Mutanen Yahuza kuma sun yawaita biranensu masu garu, Amma ni Ubangiji, zan aika da wuta a kan biranensu, Ta ƙone fādodinsu.”


Ga zantuttukan Amos, ɗaya daga cikin makiyayan ƙauyen Tekowa. Allah ya bayyana wa Amos wannan saƙo, tun shekara biyu kafin girgizar duniya, a lokacin da Azariya yake sarautar Yahuza, Yerobowam ɗan Yehowash kuwa yake sarautar Isra'ila.


Taku ta ƙare, ku da kuke zaman sakewa a Sihiyona, Da ku da kuke tsammani kuna zaman lafiya a Samariya, Ku da kuke manyan mutane Na wannan babbar al'umma ta Isra'ila, Waɗanda jama'a suke zuwa a gare su neman taimako!


Duk wannan kuwa saboda laifin Yakubu ne, Da laifin Isra'ila. Mene ne laifin Yakubu? Ashe, ba bautar gumaka da zaluncin da ake yi a Samariya ba? Mene ne kuma laifin Yahuza? Ashe, ba bautar gumaka da zaluncin da ake yi a Urushalima ba?


Ku ji wannan, ya ku shugabannin jama'ar Yakubu, Da ku sarakunan mutanen Isra'ila, Ku da kuke ƙyamar shari'ar gaskiya, Kuna karkatar da dukan gaskiya.


Jawabin da annabi Habakuk ya hurta ke nan.


Domin ba wani annabcin da ya taɓa samuwa ta nufin mutum, sai dai mutane ne Ruhu Mai Tsarki yake izawa, Allah yana magana ta bakinsu.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan