Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 9:36 - Littafi Mai Tsarki

36 Amma da ya ga taro masu yawa sai ya ji tausayinsu, domin suna shan wahala, suna nan a warwatse kamar tumaki da ba makiyayi.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

36 Da ya ga taron mutane, sai ya ji tausayinsu, domin an wulaƙanta su ba su kuma da mai taimako, kamar tumaki marasa makiyayi.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 9:36
18 Iomraidhean Croise  

Mikaiya ya ce, “Na ga mutanen Isra'ila duka a warwatse a kan tuddai kamar tumakin da ba su da makiyayi, Ubangiji kuwa ya ce, ‘Waɗannan ba su da shugaba, bari kowa ya koma gidansa lafiya.’ ”


Mikaiya kuwa ya ce, “Ina ganin dukan Isra'ilawa a warwatse bisa tsaunuka, kamar tumakin da ba su da makiyayi. Ubangiji kuma ya ce, ‘Waɗannan ba su da makiyayi, bari dukansu, kowa ya koma gidansa da salama.’ ”


“Baƙin da yake zaune a Babila za su gudu zuwa ƙasashensu, suna a warwatse kamar bareyin da suke tsere wa maharbansu, kamar tumakin da ba su da makiyayi.


“Mutanena sun zama kamar ɓatattun tumaki, Waɗanda makiyayansu suka bauɗar da su, Suka ɓata a cikin tsaunuka, Suna kai da kawowa daga wannan dutse zuwa wancan. Sun manta da shingensu.


Gama maganar shirme kan gida yake yi, Masu dūba suna ganin wahayin ƙarya, Masu mafarkai suna faɗar ƙarya, Ta'aziyyarsu ta banza ce. Domin haka mutane suna ta yawo kamar tumaki, Suna shan wahala saboda rashin makiyayi.


Gama ga shi, zan sa wani makiyayi a ƙasan nan, wanda ba zai kula da masu lalacewa ba, ko waɗanda suka warwatse, ko ya warkar da gurgu, ko ya ciyar da waɗanda suka ragu, amma zai ci naman masu ƙiba, ya farfashe kofatonsu.


mutumin da zai shugabance su cikin yaƙi, don kada taron jama'ar Ubangiji su zama kamar tumakin da ba su da makiyaya.”


Sai dai ku je wurin batattun tumakin jama'ar Isra'ila, Irm


Da ya fita daga jirgin ya ga babban taron mutane. Sai ya ji tausayinsu, ya kuma warkar da marasa lafiya a cikinsu.


Ya amsa ya ce, “Ni wurin ɓatattun tumakin jama'ar Isra'ila kaɗai aka aiko ni.”


Yesu ya kira almajiransa, ya ce, “Ina jin tausayin wannan taro, don yau kwanansu uku ke nan a guna ba su da wani abinci. Ba na kuwa so in sallame su da yunwa haka, kada su kasa a hanya.”


Da saukar Yesu sai ya ga taro mai yawa, ya kuma ji tausayinsu, domin kamar tumaki suke ba makiyayi. Ya fara koya musu abubuwa da yawa.


“Ina jin tausayin wannan taro, don yau kwanansu uku ke nan a guna, ba su da wani abinci.


Gama Babban Firist da muke da shi ba marar juyayin kasawarmu ba ne, a'a, shi ne wanda aka jarabce shi ta kowace hanya da aka jarabce mu, amma bai yi zunubi ba.


Yă kuma zamana wanda zai iya tafiyar da jahilai da sangartattu a cikin salihanci, tun da yake rarrauna ne shi ta ko'ina.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan