Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 9:35 - Littafi Mai Tsarki

35 Sai Yesu ya zazzaga dukan garuruwa da ƙauyuka, yana koyarwa a majami'unsu, yana yin bisharar Mulkin Allah, yana kuma warkar da kowace irin cuta da rashin lafiya.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

35 Yesu ya zazzaga dukan garuruwa da ƙauyuka, yana koyarwa a majami’unsu, yana wa’azin labari mai daɗi na mulkin yana kuma warkar da kowace irin cuta da rashin lafiya.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 9:35
12 Iomraidhean Croise  

Sai ya kira almajiransa goma sha biyu, ya kuma ba su ikon fitar da baƙaƙen aljannu, su warkar da kowace irin cuta da rashin lafiya.


Da Yesu ya gama yi wa almajiransa sha biyun nan umarni, sai ya ci gaba daga nan domin ya koyar, yă kuma yi wa'azi a garuruwansu.


Makafi suna samun gani, guragu suna tafiya, ana tsarkake kutare, kurame suna ji, ana ta da matattu, ana kuma yi wa matalauta bishara.


To, bayan an tsare Yahaya, sai Yesu ya shigo ƙasar Galili, yana yin bisharar Allah,


Duk inda ya shiga kuma, birni ko ƙauye ko karkara, sukan kwantar da marasa lafiya a bakin kasuwa, su roƙe shi su taɓa ko ma da gezar mayafinsa ma. Iyakar waɗanda suka taɓa shi kuwa suka warke.


Ya yi mamakin rashin bangaskiyarsu. Sai ya zazzaga ƙauyuka yana koyarwa.


Sai ya ɗauki hanyarsa ta zuwa birane da ƙauyuka, yana koyarwa, yana dosar Urushalima.


wato labarin Yesu Banazare, yadda Allah ya shafe shi da Ruhu Mai Tsarki da kuma iko, da yadda ya riƙa zagawa na aikin alheri, yana warkar da duk waɗanda Iblis ya matsa wa, domin Allah yana tare da shi.


“Ya ku 'yan'uwa, Isra'ilawa, ku ji wannan magana. Yesu Banazare, mutumin da Allah ya tabbatar muku cewa shi yardajjensa ne, ta mu'ujizai, da abubuwan al'ajabi, da alamu waɗanda ya yi ta wurinsa a cikinku, kamar yadda ku kanku kuka sani,


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan