Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 9:33 - Littafi Mai Tsarki

33 Bayan an fitar da aljanin, sai beben ya yi magana, taron kuwa suka yi mamaki, suka ce, “Kai! Ba a taɓa ganin irin wannan a cikin Isra'ila ba.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

33 Sa’ad da aka fitar da aljanin kuwa, sai beben ya yi magana. Taron suka yi mamaki suka ce, “Ba a taɓa ganin irin wannan abu a Isra’ila ba.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 9:33
12 Iomraidhean Croise  

Amma sa'ad da Elisha, annabin Allah, ya ji cewa Sarkin Isra'ila ya keta tufafinsa, sai ya aika wa sarki ya ce, “Me ya sa ka keta tufafinka? Bari ya zo wurina, zai sani akwai annabi a Isra'ila.”


Allah sananne ne a Yahuza, Mashahuri ne kuma a Isra'ila.


Gurgu zai yi tsalle ya yi rawa, Waɗanda ba su iya magana za su yi sowa don murna. Rafuffukan ruwa za su yi gudu a cikin hamada,


Ka aikata alamu da al'ajabai a ƙasar Masar. Har wa yau kuma kana aikata su a Isra'ila da kuma cikin dukan al'ummai, ka yi wa kanka suna kamar yadda yake a yau.


Da Yesu ya ji haka, sai ya yi mamaki, har ya ce wa mabiyansa, “Gaskiya, ina gaya muku, ko a cikin Isra'ila ban taɓa samun bangaskiya mai ƙarfi irin wannan ba.


Sun tashi ke nan, sai aka kawo masa wani bebe mai aljan.


Sai ya tashi nan da nan, ya ɗauki shimfiɗarsa, ya fita a gaban idon kowa, har suka yi mamaki duka, suka ɗaukaka Allah suna cewa, “Ba mu taɓa ganin irin haka ba!”


Wata rana Yesu yana fitar da beben aljan. Da aljanin ya fita, sai beben ya yi magana, taron kuwa suka yi mamaki.


Da Yesu ya ji haka, ya yi mamakinsa, ya kuma juya ya ce wa taron da suke biye da shi, “Ina gaya muku, ko a cikin Isra'ila ban taɓa samun bangaskiya mai ƙarfi irin wannan ba.”


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan