32 Sun tashi ke nan, sai aka kawo masa wani bebe mai aljan.
32 Yayinda suke fitowa, sai aka kawo wa Yesu wani mutum mai aljani, da ba ya iya magana.
Gurgu zai yi tsalle ya yi rawa, Waɗanda ba su iya magana za su yi sowa don murna. Rafuffukan ruwa za su yi gudu a cikin hamada,
Ta haka ya shahara a cikin duk ƙasar Suriya. Aka kuwa kakkawo masa dukan marasa lafiya, masu fama da cuta iri iri, da masu shan azaba, da kuma masu aljannu, da masu farraɗiya, da shanyayyu, ya kuwa warkar da su.
Wata rana Yesu yana fitar da beben aljan. Da aljanin ya fita, sai beben ya yi magana, taron kuwa suka yi mamaki.