Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 9:30 - Littafi Mai Tsarki

30 Sai idanunsu suka buɗe. Amma Yesu ya kwaɓe su ƙwarai, ya ce, “Kada fa kowa ya ji labarin.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

30 sai idanunsu suka buɗe. Yesu ya gargaɗe su sosai ya ce, “Ku lura kada wani yă san wani abu game da wannan.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 9:30
13 Iomraidhean Croise  

Yakan ba makafi ganin gari. Yakan ɗaukaka waɗanda aka wulakanta. Yana ƙaunar jama'arsa, adalai.


Makaho zai iya ganin gari, Kurma kuma zai iya ji.


Za ka buɗe idanun makafi, Ka kuma kwance waɗanda suke ɗaure a kurkuku masu duhu.


Ubangiji ya ce, “Bawana zai yi nasara a aikinsa, Zai zama babba, a kuwa girmama shi ƙwarai.


Sai ya kwaɓe su, kada su bayyana shi.


Suna cikin gangarowa daga dutsen, sai Yesu ya kwaɓe su ya ce, “Kada ku gaya wa kowa abin da kuka gani, sai an ta da Ɗan Mutum daga matattu.”


Sai Yesu ya ce masa, “Ka kula fa, kada ka gaya wa kowa kome. Sai dai ka je wurin firist ya gan ka, ka kuma yi sadaka domin tabbatarwa a gare su, kamar yadda Musa ya umarta.”


Ya kwaɓe shi ƙwarai, ya sallame shi nan da nan,


Sai ya kwaɓe su ƙwarai kada su bayyana shi.


Sai ya kwaɓe su matuƙa kada kowa ya ji wannan labari. Ya kuma yi umarni a ba ta abinci.


Yesu ya kwaɓe shi kada ya gaya wa kowa, ya ce, “Sai dai ka je wurin firist ya gan ka, ka kuma yi hadaya saboda tsarkakewarka, domin tabbatarwa a gare su, kamar yadda Musa ya umarta.”


Iyayenta suka yi mamaki. Amma ya kwaɓe su kada su gaya wa kowa abin da ya faru.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan