21 domin ta ce a ranta, “Ko da mayafinsa ma na taɓa, sai in warke.”
21 Ta ce a ranta, “Ko da rigarsa ce kawai na taɓo, zan warke.”
suka roƙe shi su taɓa ko da gezar mayafinsa ma, iyakar waɗanda suka taɓa kuwa suka warke.
saboda ya riga ya warkar da mutane da yawa, har ya kai ga duk masu cuta na dannowa wurinsa domin su taɓa shi.
Duk taron suka nema su taɓa shi, domin iko yana fitowa daga gare shi, ya kuwa warkar da su duka.
har akan kai wa marasa lafiya adikansa, ko tufafinsa da yake sawa yana aiki, sun kuwa warke daga cuce-cucensu, baƙaƙen aljannu kuma sun rabu da su.