Yana cikin yi musu magana haka, sai ga wani shugaban jama'a ya zo, ya yi masa sujada, ya ce, “Yanzu yanzu 'yata ta rasu, amma ka zo ka ɗora mata hannu, za ta rayu.”
wato labarin Yesu Banazare, yadda Allah ya shafe shi da Ruhu Mai Tsarki da kuma iko, da yadda ya riƙa zagawa na aikin alheri, yana warkar da duk waɗanda Iblis ya matsa wa, domin Allah yana tare da shi.