Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 9:18 - Littafi Mai Tsarki

18 Yana cikin yi musu magana haka, sai ga wani shugaban jama'a ya zo, ya yi masa sujada, ya ce, “Yanzu yanzu 'yata ta rasu, amma ka zo ka ɗora mata hannu, za ta rayu.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

18 Yayinda yake faɗin wannan, sai wani mai mulki ya zo ya durƙusa a gabansa ya ce, “Yanzu-yanzu diyata ta rasu. Amma ka zo ka ɗibiya hannunka a kanta, za tă kuwa rayu.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 9:18
25 Iomraidhean Croise  

Amma Na'aman ya husata, ya yi tafiyarsa, yana cewa, “Na yi tsammani zai fito ya zo wurina ne, ya tsaya, ya yi kira sunan Ubangiji Allahnsa ya kaɗa hannunsa a wurin kuturtar, ya warkar da ni.


Na cikin jirgin suka yi masa sujada, suka ce, “Hakika kai Ɗan Allah ne.”


Amma ta zo ta durƙusa a gabansa, ta ce, “Ya Ubangiji, ka taimake ni mana!”


Da suka isa wurin taro, sai wani mutum ya zo gare shi, ya durƙusa a gabansa, ya ce,


Sa'an nan uwar 'ya'yan Zabadi ta matso wurinsa tare da 'ya'yanta, ta durƙusa a gabansa, ta roƙe shi wani abu.


Da suka gan shi, suka yi masa sujada, amma waɗansu suka yi shakka.


Sai ga wani kuturu ya zo gunsa ya yi masa sujada, ya ce, “Ya Ubangiji, in dai ka yarda, kana da iko ka tsarkake ni.”


Sai almajiransa suka je suka tashe shi, suka ce, “Ya Ubangiji, ka cece mu, za mu hallaka!”


Ba kuma mai ɗura sabon ruwan inabi a tsofaffin salkuna. In ma an ɗura, sai salkunan su fashe, ruwan inabin ya zube, salkunan kuma su lalace. Sabon ruwan inabi, ai, sai sababbin salkuna. Ta haka an tserar da duka biyu ke nan.”


Sai Yesu ya tashi, ya bi shi tare da almajiransa.


sai ya ce, “Ku ba da wuri, ai, yarinyar ba matacciya take ba, barci take yi.” Sai suka yi masa dariyar raini.


Amma shugaban majami'a ya ji haushi, don Yesu ya warkar ran Asabar. Sai ya ce wa jama'a, “Akwai ranaku har shida da ya kamata a yi aiki. Ku zo mana a ranakun nan a warkar da ku, ba ran Asabar ba.”


Wani shugaban jama'a ya tambaye shi ya ce, “Malam managarci, me zan yi in gaji rai madawwami?”


To, sai bawan wani jarumi, wanda Ubangijinsa yake jin daɗinsa, ya yi rashin lafiya, har ya kai ga bakin mutuwa.


Yesu ya ce mata, “Ai, ni ne tashin matattu, ni ne kuma rai. Wanda ya gaskata da ni, ko ya mutu zai rayu.


Da Maryamu ta iso inda Yesu yake, ta gan shi, sai ta faɗi a gabansa ta ce masa, “Ya Ubangiji, da kana nan da dan'uwana bai mutu ba.”


Bayan an yi karatun Attaura da littattafan annabawa, shugabannin majami'ar suka aika musu, suka ce, “'Yan'uwa, in kuna da wata maganar gargaɗi da za ku yi wa jama'a, ai, sai ku yi.”


Ashe, uban Babiliyas yana a kwance, yana fama da zazzaɓi da atuni. Sai Bulus ya shiga wurinsa ya yi addu'a, ya ɗora masa hannu ya warkar da shi.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan