Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 9:15 - Littafi Mai Tsarki

15 Sai Yesu ya ce musu, “Abokan ango sa yi baƙin ciki tun ango yana tare da su? Ai, lokaci yana zuwa da za a ɗauke musu angon. A sa'an nan ne fa za su yi azumi.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

15 Yesu ya amsa ya ce, “Yaya baƙin ango za su yi makoki yayinda yake tare da su? Lokaci yana zuwa da za a ɗauke ango daga gare su, sa’an nan za su yi azumi.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 9:15
22 Iomraidhean Croise  

Ubangiji Mai Runduna yana kiranku ku yi kuka, ku yi makoki, ku aske kawunanku, ku sa tsummoki.


Sai almajiran Yahaya suka zo wurinsa, suka ce, “Don me mu da Farisiyawa mukan yi azumi, amma naka almajiran ba sa yi?”


Ba mai mahon tsohuwar tufa da sabon ƙyalle, don mahon zai kece tsohuwar tufar, har ma ta fi dā kecewa.


Sai Yesu ya ce musu, “Ashe, abokan ango sa iya azumi tun ango na tare da su? Ai, muddin suna tare da angon, ba za su yi azumi ba.


Ai, lokaci na zuwa da za a ɗauke musu angon. A sa'an nan ne fa za su yi azumi.


Ya kuma ce wa almajiran, “Lokaci na zuwa da za ku yi begen ganin rana ɗaya daga cikin ranakun Ɗan Mutum, amma ba za ku gani ba.


Sai Yesu ya ce musu, “Wato kwa iya sa abokan ango su yi azumi tun angon yana tare da su?


Ai, lokaci na zuwa da za a ɗauke musu angon. A sa'an nan ne fa za su yi azumi.”


Amma saboda na faɗa muku waɗannan abubuwa, ga shi baƙin ciki ya cika zuciyarku.


Mai amarya shi ne ango. Abokin ango kuwa da yake tsaye, yake kuma sauraron magana tasa, yakan yi farin ciki ƙwarai da jin muryar angon. Saboda haka farin cikin nan nawa ya cika.


Bayan kuma sun zaɓar musu dattawa a kowace Ikkilisiya, game da addu'a da azumi, suka danƙa su ga Ubangiji, wanda dā ma suka gaskata da shi.


Kada ɗayanku yă ƙaurace wa ɗaya, sai ko da yardar juna zuwa wani ɗan lokaci kaza, don ku himmantu ga addu'a, sa'an nan ku sāke haɗuwa, kada Shaiɗan yă zuga ku ta wajen rashin kamewa.


Na sha fama, na sha wuya, na sha rashin barci, na sha yunwa da ƙishirwa, sau da yawa na rasa abinci, na sha sanyi da huntanci.


Sai mala'ikan ya ce mini, “Rubuta wannan, ‘Albarka tā tabbata ga waɗanda aka gayyata, zuwa cin abincin bikin Ɗan Ragon nan.’ ” Ya kuma ce mini, “Wannan ita ce Maganar Allah ta gaskiya.”


Sai na ga tsattsarkan birni kuma, Sabuwar Urushalima, tana saukowa daga Sama daga wurin Allah, shiryayyiya kamar amaryar da ta yi ado saboda mijinta.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan