Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 9:13 - Littafi Mai Tsarki

13 Sai ku fahimci ma'anar wannan tukuna, ‘Ni kam, zaman jinƙai nake nema a gare ku, ba hadaya ba.’ Ba domin in kira masu adalci na zo ba, sai dai masu zunubi.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

13 Amma ku je ku koyi abin da wannan yake nufi, ‘Jinƙai nake bukata, ba hadaya ba.’ Gama ban zo domin in kira masu adalci ba, sai dai masu zunubi.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 9:13
39 Iomraidhean Croise  

Ubangiji ya fi so ka yi abin da yake daidai, mai kyau kuma, fiye da ka miƙa masa hadayu.


Gama ƙauna nake so, ba sadaka ba, Sanin Allah kuma fiye da hadayu na ƙonawa.


Sai ya ce musu, “Ashe, ba ku taɓa karanta abin da Dawuda ya yi ba sa'ad da ya ji yunwa, shi da abokan tafiyarsa?


Ko kuwa ba ku taɓa karantawa a Attaura ba, yadda a ran Asabar, firistoci a Haikalin sukan keta dokar Asabar, ba tare da yin wani laifi ba kuwa?


Da kun san ma'anar wannan cewa, ‘Ni kam, zaman jinƙai nake nema a gare ku, ba hadaya ba’, da ba ku ga laifin marasa laifi ba.


Ya amsa ya ce, “Ashe, ba ku taɓa karantawa ba, cewa, wanda ya halicce su tun farko, dā ma ya yi su, namiji da tamata?”


Yesu ya ce musu, “Ashe, ba ku taɓa karantawa a Littattafai ba? cewa, “ ‘Dutsen da magina suka ƙi, Shi ne ya zama mafificin dutsen gini. Wannan aikin Ubangiji ne, A gare mu kuwa abin al'ajabi ne.’


yana cewa, “Ku tuba, domin Mulkin Sama ya kusato.”


Ku yi aikin da zai nuna tubarku.


Tun daga lokacin nan, Yesu ya fara wa'azi, yana cewa, “Ku tuba domin Mulkin Sama ya kusato.”


Game da tashin matattu kuma, ashe, ba ku taɓa karantawa a Littafin Musa ba, yadda Allah ya ce masa, ‘Ni ne Allahn Ibrahim, da Ishaku, da kuma Yakubu’?


A ƙaunace shi kuma da dukkan zuciya, da dukan hankali, da dukkan ƙarfi, a kuma ƙaunaci ɗan'uwa kamar kai, ai, ya fi dukkan hadayar ƙone-ƙone da yanke-yanke nesa.”


Da Yesu ya ji haka, ya ce musu, “Ai, lafiyayyu ba ruwansu da likita, sai dai marasa lafiya. Ba domin in kira masu adalci na zo ba, sai masu zunubi.”


Yesu ya ce musu, “Me yake rubuce a Attaura? Yaya kake karantawa?”


Don Ɗan Mutum ya zo ne musamman garin neman abin da ya ɓata, yă cece shi kuma.”


a kuma yi wa dukan al'ummai wa'azi su tuba, a gafarta musu zunubansu saboda sunansa. Za a kuwa fara daga Urushalima.


Yesu ya amsa musu ya ce, “Ai, lafiyayyu ba ruwansu da magani, sai dai marasa lafiya.


Ba domin in kira masu adalci na zo ba, sai dai masu zunubi, su tuba.”


Yesu ya amsa musu ya ce, “Ba a rubuce yake a Shari'arku ba cewa, ‘Na ce ku alloli ne’?


Da suka ji haka, suka rasa ta cewa, suka kuma ɗaukaka Allah suka ce, “Ashe, har al'ummai ma Allah ya ba su tuba zuwa rai.”


Sai Bitrus ya ce musu, “Sai ku tuba, a yi wa ko wannenku baftisma, a kan kun yarda da sunan Yesu Almasihu, domin a gafarta zunubanku, za ku kuwa sami baiwar Ruhu Mai Tsarki,


ina tabbatar wa Yahudawa da al'ummai duka sosai wajibcin tuba ga Allah, da kuma gaskatawa da Ubangijinmu Yesu.


Saboda haka sai ku tuba, ku juyo, domin a shafe zunubanku, Ubangiji kuma kansa ya riƙa wartsakar da ku,


Shi ne Allah ya ɗaukaka ga damansa, Shugaba da kuma Mai Ceto, domin ya buɗe wa Isra'ila hanyar tuba, su kuma sami gafarar zunubansu.


Ubangiji ba ya jinkirta alkawarinsa, yadda waɗansu suka ɗauki ma'anar jinkiri, amma mai haƙuri ne a gare ku, ba ya so kowa ya hallaka, sai dai kowa ya kai ga tuba.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan