Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 9:12 - Littafi Mai Tsarki

12 Amma da Yesu ya ji haka ya ce, “Ai, lafiyayyu ba ruwansu da likita, sai dai marasa lafiya.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

12 Da jin wannan, Yesu ya ce, “Ai, ba masu lafiya ba ne su bukatar likita, sai dai marasa lafiya.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 9:12
17 Iomraidhean Croise  

Yakan warkar da masu karyayyiyar zuciya, Yakan ɗaure raunukansu.


Na ce, “Na yi maka zunubi, ya Ubangiji, Ka yi mini jinƙai ka warkar da ni!”


Ka ji tausayina, gama na gaji tiƙis, Ka wartsarkar da ni, gama na tafke sarai.


Ubangiji, ka warkar da ni, zan kuwa warke, Ka cece ni, zan kuwa cetu, Gama kai ne abin yabona.


Zan mayar muku da lafiyarku, Zan kuma warkar da raunukanku, Ko da yake maƙiyanku suna kiranku yasassu, Suna cewa, ‘Ai, Sihiyona ce, ba wanda ya kula da ita.’ Ni Ubangiji na faɗa.”


Ga shi, zan kawo wa birnin lafiya, gama zan warkar da su, in wadata su da salama da gaskiya.


Ba abin sanyayawa a Gileyad ne? Ba mai magani a can ne? Me ya sa ba a warkar da jama'ata ba?


Ubangiji ya ce, “Zan warkar musu da riddarsu. Zan kuma ƙaunace su sosai, Gama fushina zai huce.


[Domin Ɗan Mutum ya zo ne musamman ceton abin da ya ɓata.]


Da Yesu ya ji haka, ya ce musu, “Ai, lafiyayyu ba ruwansu da likita, sai dai marasa lafiya. Ba domin in kira masu adalci na zo ba, sai masu zunubi.”


Yesu ya amsa musu ya ce, “Ai, lafiyayyu ba ruwansu da magani, sai dai marasa lafiya.


sai ga wata mace wadda ta shekara goma sha biyu tana zub da jini, ta kuma ɓad da duk abin hannunta wajen masu magani, ba wanda ya iya warkar da ita.


Ganin haka sai taro masu yawa suka bi shi. Ya kuwa yi musu maraba, ya yi musu maganar Mulkin Allah, ya kuma warkar da masu bukatar warkewa.


Luka, ƙaunataccen likitan nan, da Dimas suna gaishe ku.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan