Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 8:8 - Littafi Mai Tsarki

8 Sai jarumin, ya ce, “Ya Ubangiji, ban isa har ka zo gidana ba, amma sai ka yi magana kawai, yarona kuwa zai warke.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

8 Jarumin ya amsa, “Ubangiji, ban cancanci in sa ka zo gidana ba, ka dai yi magana kawai, bawana zai warke.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 8:8
18 Iomraidhean Croise  

ban cancanci ayyukanka na ƙauna da irin amincin da ka gwada wa baranka ba, gama da sandana kaɗai na haye Kogin Urdun, ga shi yanzu kuwa na zama ƙungiya biyu.


Za ka saurara ga addu'o'in masu kaɗaici, ya Ubangiji, Za ka ba su ƙarfin hali.


Da umarninsa ya warkar da su, Ya cece su daga kabari.


Da magana ya halicci duniya, Ta wurin umarninsa kowane abu ya bayyana.


“Ka ɗauki sandanka, kai da Haruna, ɗan'uwanka, ku tara jama'a, ku yi magana da dutsen a gabansu ya ba da ruwan da yake cikinsa. Za ka sa ruwa ya ɓuɓɓugo musu daga dutsen. Ta haka za ka ba taron jama'a da garkunansu ruwan sha.”


“Ni dai, da ruwa nake muku baftisma, shaidar tubarku, amma mai zuwa bayana, ya fi ni girma, wanda ko takalmansa ma ban isa in riƙe ba. Shi ne zai yi muku baftisma da Ruhu Mai Tsarki, da kuma wuta.


Yahaya kuwa ya so ya hana shi, ya ce, “Ni da nake bukatar kai ka yi mini baftisma, ka zo gare ni?”


Sai Yesu ya miƙa hannu, ya taɓa shi, ya ce, “Na yarda, ka tsarkaka.” Nan take kuturtarsa ta warke.


Yesu ya ce masa, “Zan zo in warkar da shi.”


Don ni ma a hannun wani nake, da kuma soja a hannuna, sai in ce wa wannan, ‘Je ka,’ sai ya je, wani kuwa in ce masa, ‘Zo,’ sai ya zo, in ce wa bawana, ‘Yi abu kaza,’ sai ya yi.”


Ban ma cancanci a ƙara kirana ɗanka ba. Ka mai da ni kamar ɗaya daga cikin barorinka.” ’


Sai kuma ɗan ya ce masa, ‘Baba, na yi wa Mai Sama zunubi, na kuma saɓa maka. Ban ma cancanci a ƙara kirana ɗanka ba.’


Da Bitrus ya ga haka, sai ya fāɗi a gaban Yesu ya ce. “Ya Ubangiji, wane ni da za ka tsaya kusa da ni, domin ni mutum ne mai zunubi.”


shi ne mai zuwa bayana, wanda ko maɓallin takalminsa ma, ban isa in ɓalle ba.”


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan