Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 8:6 - Littafi Mai Tsarki

6 ya ce, “Ya Ubangiji, yarona na kwance a gida, ya zama shanyayye, yana shan azaba ƙwarai.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

6 Ya ce, “Ubangiji, bawana yana kwance a gida shanyayye, yana kuma shan azaba ƙwarai.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 8:6
12 Iomraidhean Croise  

Ta haka ya shahara a cikin duk ƙasar Suriya. Aka kuwa kakkawo masa dukan marasa lafiya, masu fama da cuta iri iri, da masu shan azaba, da kuma masu aljannu, da masu farraɗiya, da shanyayyu, ya kuwa warkar da su.


Yesu ya ce masa, “Zan zo in warkar da shi.”


Sai aka kawo masa wani shanyayye, kwance a gado. Da Yesu ya ga bangaskiyarsu, sai ya ce wa shanyayyen, “Ɗana, ka yi farin ciki, an gafarta maka zunubanka.”


Da mala'ikan da ya yi masa magana ya tafi, ya kira barorinsa biyu, da kuma wani soja mai ibada daga cikin waɗanda suke yi masa hidima kullum.


Domin da yawa masu baƙaƙen aljannu suka rabu da su, aljannun kuwa na ta ihu. Shanyayyu da guragu da yawa kuma an warkar da su.


Nan ya tarar da wani mutum, mai suna Iniyasu, wanda yake kwance a kan gado shekara takwas, yana shanyayye.


A nan kam, ba hanyar nuna bambanci a tsakanin Ba'al'umme da Bayahude, ko mai kaciya da marar kaciya, ko bare da baubawa, ko ɗa da bawa, sai dai Almasihu shi ne kome, shi kuma yake cikinmu duka.


Ku iyayengiji kuma, ku riƙi bayinku da gaskiya da daidaita, da yake kun sani ku ma kuna da Ubangiji a Sama.


Waɗanda suke da iyayengiji masu ba da gaskiya, kada su raina su, domin su 'yan'uwa ne a gare su. Sai ma su ƙara bauta musu, tun da yake waɗanda suke moron aikin nan nasu masu ba da gaskiya ne, ƙaunatattu kuma a gare su. Ka koyar da waɗannan abubuwa, ka kuma yi gargaɗinsu.


ba kuma a kan bawa ba, sai dai a kan abin da ya fi bawa, wato 'dan'uwa abin ƙauna, tun ba ma a gare ni ba, balle fa a gare ka, ta wajen al'amarin jiki da kuma wajen al'amarin Ubangiji.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan