Ke kuma Kafarnahum, ɗaukaka ki sama za a yi? A'a, ƙasƙantar da ke za a yi, har Hades. Da mu'ujizan da aka yi a cikinki, su aka yi a Saduma, da ta wanzu har ya zuwa yau.
Sa'ad da jarumin da waɗanda suke tare da shi suna tsaron Yesu suka ga rawar ƙasa da kuma abin da ya auku, sai duk tsoro ya kama su, suka ce, “Hakika wannan Ɗan Allah ne!”
Bayan sun ɗaɗɗaure shi da tsirkiya, Bulus ya ce wa jarumin ɗin da yake tsaye kusa, “Ashe, ya halatta a gare ka ka yi wa mutumin da yake da 'yancin Roma bulala, ba ko bin ba'asi?”