Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 8:4 - Littafi Mai Tsarki

4 Sai Yesu ya ce masa, “Ka kula fa, kada ka gaya wa kowa kome. Sai dai ka je wurin firist ya gan ka, ka kuma yi sadaka domin tabbatarwa a gare su, kamar yadda Musa ya umarta.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

4 Sai Yesu ya ce masa, “Ka lura kada ka gaya wa kowa. Sai dai ka tafi, ka nuna kanka ga firist ka kuma yi bayarwar da Musa ya umarta, a matsayin shaida gare su.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 8:4
31 Iomraidhean Croise  

Ubangiji shi Allah ne da ya ƙosa ya yi ceto saboda gaskiyarsa, Saboda haka yana so a girmama koyarwarsa,


idan cutar ta zama kore-kore, ko jaja-jaja a rigar, ko a fatar, ko a tariyar zaren, ko a waɗarin, ko a kan abin da aka yi da fata, wannan cuta kuturta ce, sai a nuna wa firist.


Za su kuma ja ku gaban mahukunta da sarakuna saboda ni, domin ku ba da shaida a gabansu, a gaban al'ummai kuma.


Sai ya kwaɓi almajiransa ƙwarai kada su gaya wa kowa shi ne Almasihu.


Suna cikin gangarowa daga dutsen, sai Yesu ya kwaɓe su ya ce, “Kada ku gaya wa kowa abin da kuka gani, sai an ta da Ɗan Mutum daga matattu.”


Amma Yesu ya amsa masa ya ce, “Bari ya zama haka a yanzu, domin haka ne ya dace mu cika dukan adalci.” Sa'an nan Yahaya ya yardar masa.


“Kada ku yi zaton na zo ne in shafe Attaura da koyarwar annabawa. Na zo ne ba domin in shafe su ba, sai dai domin in cika su.


“Ku yi hankali kada ibadarku ta zama ta ganin ido. Domin in kun yi haka, ba za ku sami sakamako wurin Ubanku da yake a Sama ba.


Sai idanunsu suka buɗe. Amma Yesu ya kwaɓe su ƙwarai, ya ce, “Kada fa kowa ya ji labarin.”


“Amma ku kula da kanku, don za su kai ku gaban majalisa, a kuma yi muku dūka a majami'u. Za a kuma kai ku gaban mahukunta da sarakuna saboda sunana, domin ku ba da shaida a gabansu.


Sai ya kwaɓe su ƙwarai kada su bayyana shi.


Sai ya kwaɓe su matuƙa kada kowa ya ji wannan labari. Ya kuma yi umarni a ba ta abinci.


Duk inda aka ƙi yin na'am da ku, aka kuma ƙi sauraronku, in za ku tashi, sai ku karkaɗe ƙurar ƙafafunka don shaida a kansu.”


Yesu ya kwaɓe su kada su faɗa wa kowa, amma ƙara yawan kwaɓonsu ƙara yawan yaɗa labarin.


Sai ya kwaɓe su kada su gaya wa kowa labarinsa.


Suna cikin gangarowa daga dutsen, sai ya kwaɓe su kada su gaya wa kowa abin da suka gani, sai bayan Ɗan Mutum ya tashi daga matattu.


Da ya gan su, ya ce musu, “Ku je wurin firistoci su gan ku.” Suna tafiya ke nan, sai suka tsarkaka.


Wannan zai zama muku hanyar ba da shaida.


Aljannu kuma suka fita daga mutane da yawa, suna ihu suna cewa, “Kai Ɗan Allah ne!” Amma ya tsawata musu, ya hana su magana, don sun sani shi ne Almasihu.


Yesu ya kwaɓe shi kada ya gaya wa kowa, ya ce, “Sai dai ka je wurin firist ya gan ka, ka kuma yi hadaya saboda tsarkakewarka, domin tabbatarwa a gare su, kamar yadda Musa ya umarta.”


Iyayenta suka yi mamaki. Amma ya kwaɓe su kada su gaya wa kowa abin da ya faru.


Sai ya kwaɓe su gaya matuƙa kada su gaya wa kowa wannan magana.


Ba na karɓar girma wurin mutane.


Mai magana don kansa, neman ɗaukakar kansa yake yi. Amma mai neman ɗaukakar wanda ya aiko shi, shi ne mai gaskiya, ba kuwa rashin gaskiya a gare shi.


Ba ni nake nemar wa kaina girma ba, akwai mai nemar mini, shi ne kuma mai yin shari'a.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan