Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 8:3 - Littafi Mai Tsarki

3 Sai Yesu ya miƙa hannu, ya taɓa shi, ya ce, “Na yarda, ka tsarkaka.” Nan take kuturtarsa ta warke.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

3 Yesu ya miƙa hannunsa ya taɓa mutumin. Ya ce, “Ina so, ka tsabtacce!” Nan da nan aka warkar da shi daga kuturtarsa.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 8:3
19 Iomraidhean Croise  

Allah ya ce, “Bari haske ya kasance,” sai kuwa ya kasance.


Amma Na'aman ya husata, ya yi tafiyarsa, yana cewa, “Na yi tsammani zai fito ya zo wurina ne, ya tsaya, ya yi kira sunan Ubangiji Allahnsa ya kaɗa hannunsa a wurin kuturtar, ya warkar da ni.


Sai ya tafi ya yi wanka har sau bakwai a Kogin Urdun bisa ga maganar annabin Allah, sai naman jikinsa ya warke ya zama kamar na ƙaramin yaro, ya tsarkaka.


Da magana ya halicci duniya, Ta wurin umarninsa kowane abu ya bayyana.


Allah kuma ya ce masa, “Mai da hannunka cikin ƙirjinka.” Sai ya mai da hannunsa cikin ƙirjinsa. Sa'ad da ya fitar da shi, ga hannun ya koma kamar sauran jikinsa.


Sa'an nan ya ce wa mutumin, “Miƙo hannunka.” Ya miƙa. Sai ya koma lafiyayye kamar ɗayan.


Da tausayi ya kama Yesu, sai ya miƙa hannu, ya taɓa shi, ya ce masa, “Na yarda, ka tsarkaka.”


Sai ya farka, ya tsawata wa iskar, ya kuma ce wa ruwan tekun, “Natsu! Ka yi shiru!” Sai iskar ta kwanta, wurin duk ya yi tsit.


Ya kama hannunta, ya ce mata, “Talita ƙumi”, wato, “Ke yarinya, ina ce miki, tashi.”


Ya ɗaga kai sama ya yi ajiyar zuciya, sai ya ce masa, “Iffata!” wato “Buɗu!”


Da Yesu ya ga taro na ɗungumowa a guje, sai ya tsawata wa baƙin aljanin ya ce masa, “Kai, beben aljan, na umarce ka ka rabu da shi, kada kuma ka ƙara hawansa.”


A zamanin Annabi Elisha kuma akwai kutare da yawa a Isra'ila, ba kuwa ɗayansu da aka tsarkake sai Na'aman, mutumin Suriya, kaɗai.”


Sai Yesu ya miƙa hannu, ya taɓa shi, ya ce, “Na yarda, ka tsarkaka.” Nan take sai kuturtar ta rabu da shi.


Sa'an nan ya matso, ya taɓa makarar, masu ɗauka kuma suka tsaya cik. Sai Yesu ya ce, “Samari, na ce maka ka tashi.”


Da ya faɗi haka ya ɗaga murya da ƙarfi ya ce, “Li'azaru fito!”


Da ba domin na yi ayyuka a cikinsu da ba wanda ya taɓa yi sai ni ba, da ba su da zunubi. Amma yanzu sun gani, sun kuma ƙi mu, ni da Ubana duka.


Yadda Uba yake ta da matattu ya kuma raya su, haka Ɗan ma yake rayar da wanda ya nufa.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan