Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 8:29 - Littafi Mai Tsarki

29 Sai suka ƙwala ihu suka ce, “Ina ruwanka da mu, kai Ɗan Allah? Ka zo nan ne ka yi mana azaba tun kafin lokaci ya yi?”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

29 Suka yi ihu suka ce, “Me ya haɗa ka da mu, Ɗan Allah?” Ka zo ne nan don ka ji mana kafin lokaci yă yi?

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 8:29
20 Iomraidhean Croise  

Amma sarki ya ce masa, “Ba ruwanku, ku 'ya'yan Zeruya. Idan yana zagi saboda Ubangiji ya sa shi, to, wa ya isa ya ce, ‘Don me kake yin haka?’ ”


Amma Dawuda ya ce wa Abishai da ɗan'uwansa Yowab, “Ina ruwana da ku, ku 'ya'yan Zeruya? Kuna so ku jawo mini wahala? Ni ne Sarkin Isra'ila yanzu, don haka ba Ba'isra'ilen da za a kashe a yau.”


Sai macen ta ce wa Iliya, “Me ya haɗa ni da kai, ya mutumin Allah? Ka zo don ka nuna wa Allah zunubina, ka zama sanadin mutuwar ɗana?”


Elisha kuwa ya ce wa Sarkin Isra'ila, “Ina ruwana da kai? Tafi wurin annabawan tsohonka da na tsohuwarka.” Amma Sarkin Isra'ila ya ce masa, “A'a, ai, Ubangiji ya kirawo mu, mu sarakunan nan uku, domin ya bashe mu a hannun Mowabawa.”


Amma Neko ya aika 'yan saƙo su faɗa masa su ce, “Me ya gama mu da juna, ya Sarkin Yahuza? Ban zo in yi yaƙi da kai ba. Na zo ne in yi yaƙi da Sarkin Assuriya! Ka ƙyale ni! Allah ne ya riga ya faɗa mini in hanzarta. Kada ka yi gāba da Allah, wanda yake tare da ni, don kada ya hallaka ka.”


“Taya da Sidon, da dukan Filistiya, me kuke so ku yi mini? Kuna ƙoƙari ku rama mini saboda wani abu? Idan haka ne, zan rama muku da gaggawa.


Sai Mai Gwadawar nan ya zo, ya ce masa, “In kai Ɗan Allah ne, ka umarci duwatsun nan su zama gurasa.”


Nesa kuma kaɗan akwai wani babban garken alade na kiwo.


yana cewa, “Ina ruwanka da mu, Yesu Banazare? Ka zo ne ka hallaka mu? Na san ko wane ne kai, Mai Tsarkin nan ne kai na Allah.”


Baƙaƙen aljannu kuwa, duk sa'ad da suka gan shi, sai su fāɗi gabansa suna kururuwa, suna cewa, “Kai Ɗan Allah ne.”


ya ƙwala ihu ya ce, “Ina ruwanka da ni, Yesu Ɗan Allah Maɗaukaki? Na gama ka da Allah, kada ka yi mini azaba.”


“Wayyo! Ina ruwanka da mu, Yesu Banazare? Ka zo ne ka hallaka mu? Na san ko wane ne kai, Mai Tsarkin nan ne kai na Allah.”


Aljannu kuma suka fita daga mutane da yawa, suna ihu suna cewa, “Kai Ɗan Allah ne!” Amma ya tsawata musu, ya hana su magana, don sun sani shi ne Almasihu.


Da ganin Yesu sai ya ƙwala ihu, ya faɗi a gabansa, ya ɗaga murya ya ce, “Ina ruwanka da ni, ya Yesu Ɗan Allah Maɗaukaki? Ina roƙonka, kada ka yi mini azaba.”


Yesu ya ce mata, “Iya, ai, wannan magana ba taki ba ce. Lokacina bai yi ba tukuna.”


Sai ta riƙa binmu, mu da Bulus, tana ihu tana cewa, “Mutanen nan fa bayin Allah Maɗaukaki ne, suna kuwa sanar da ku hanyar ceto!”


Ka gaskata Allah ɗaya ne? To, madalla. Ai, ko aljannu ma sun gaskata, amma suna rawar jiki don tsoro.


Da yake Allah bai rangwanta wa mala'iku ba sa'ad da suka yi zunubi, sai ya jefa su a Gidan Wuta, ya tura su a cikin ramummuka masu zurfi, masu baƙin duhu, a tsare su har ya zuwa ranar hukunci,


Har ma mala'ikun da ba su kiyaye girmansu ba, amma suka bar ainihin mazauninsu, ya tsare su cikin sarƙa madawwamiya a baƙin duhu, har ya zuwa shari'ar babbar ranar nan.


Yefta kuwa ya aiki jakadu wurin Sarkin Ammonawa da cewa, “Me ya haɗa ka da ni, da ka zo ƙasata da yaƙi?”


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan