Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 8:26 - Littafi Mai Tsarki

26 Ya ce musu, “Don me kuka firgita haka, ya ku masu ƙarancin bangaskiya?” Sa'an nan ya tashi, ya tsawata wa iskar da ruwan. Sai wurin duk ya yi tsit!

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

26 Ya amsa ya ce, “Ku masu ƙarancin bangaskiya, me ya sa kuke tsoro haka?” Sa’an nan ya tashi ya tsawata wa iskar da kuma raƙuman ruwan, sai wuri ya yi tsit gaba ɗaya.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 8:26
24 Iomraidhean Croise  

Kakan kwantar da rurin tekuna, Kakan kwantar da rurin igiyar ruwa, Kakan kwantar da tarzomar jama'a.


Kai kake mulkin haukan teku, Kakan kwantar da haukan raƙuman ruwa.


Ina Ubangiji yake wanda ya yi manyan al'amura da ikonsa ta wurin Musa, ya raba ruwan teku a gaban jama'arsa, domin ya yi wa kansa madawwamin suna?”


Yakan tsauta wa teku, sai teku ta ƙafe. Yakan busar da koguna duka. Bashan da Karmel sukan bushe, Tohon Lebanon yakan yanƙwane.


Ya Ubangiji, ka hasala da koguna ne? Ko kuwa ka yi fushi da koguna? Ko kuwa ka hasala da teku ne, Sa'ad da ka hau dawakanka, kana bisa karusarka ta nasara?


Da Yesu ya lura da haka sai ya ce, “Ya ku masu ƙarancin bangaskiya, don me kuke magana da juna a kan ba ku zo da gurasa ba?


Ya ce musu, “Saboda ƙarancin bangaskiyarku. Domin hakika ina gaya muku, da kuna da bangaskiya, ko misalin ƙwayar mustad, da za ku ce wa dutsen nan, ‘Kawu daga nan, ka koma can!’, sai kuwa ya kawu. Ba kuwa abin da zai gagare ku.


To, ga shi, Allah yana ƙawata tsire-tsiren jeji ma haka, waɗanda yau suke raye, gobe kuwa a jefa su a murhu, balle ku? Ya ku masu ƙarancin bangaskiya!


Mutanen suka yi al'ajabi, suka ce, “Wane irin mutum ne wannan, wanda har iska da ruwan teku ma suke masa biyayya?”


Sai Yesu ya kwaɓe shi ya ce, “Shiru! Rabu da shi!” Bayan da aljanin ya fyaɗa shi ƙasa a tsakiyarsu, ya rabu da shi, bai kuwa cuce shi ba.


Ba kuwa wata rashin bangaskiyar da ta sa shi shakkar cikar alkawarin Allah, sai ma ƙara ƙarfafa ga bangaskiyarsa ya yi, yana ɗaukaka Allah,


Ga wani ƙaramin littafi a buɗe a hannunsa. Sai ya tsai da ƙafarsa ta dama a kan teku, ƙafarsa ta hagu kuwa a kan ƙasa,


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan