22 Amma Yesu ya ce masa, “Bi ni. Bari matattu su binne 'yan'uwansu matattu.”
22 Amma Yesu ya ce masa, “Ka bi ni, ka bar matattu su binne matattunsu.”
Sai ya bar shanun noma, ya sheƙa gun Iliya, ya ce, “Bari in sumbaci mahaifina da mahaifiyata, in yi bankwana da su, sa'an nan in zo in bi ka.” Sa'an nan Iliya ya ce masa, “Koma, me na yi maka?”
Sai ɗaya daga almajiran ya ce masa, “Ya Ubangiji, ka bar ni tukuna in je in binne tsohona.”
Da Yesu ya yi gaba, ya ga wani mutum mai suna Matiyu a zaune, yana aiki a wurin karɓar haraji. Ya ce masa, “Bi ni.” Sai ya tashi ya bi shi.
Yana cikin wucewa, sai ya ga Lawi ɗan Halfa a zaune yana aiki a wurin karɓar haraji. Yesu ya ce masa, “Bi ni.” Sai ya tashi ya bi shi.
Don ɗan nan nawa dā ya mutu ne, amma a yanzu ya komo, dā ya ɓata, amma a yanzu an same shi.’ Sai suka yi ta farin ciki.
Ai kuwa, daidai ne a yi ta murna da farin ciki, don ɗan'uwan nan naka dā ya mutu, a yanzu ya komo, dā ya ɓata, amma an same shi.’ ”
Ya kuma ce wa wani, “Bi ni.” Sai ya ce, “Ya Ubangiji, ka bar ni tukuna in je in binne tsohona.”
Sai Yesu ya ce masa, “Bari matattu su binne 'yan'uwansu matattu. Amma kai kuwa, tafi ka sanar da Mulkin Allah.”
Kashegari Yesu ya yi niyyar zuwa ƙasar Galili. Sai ya sami Filibus, ya ce masa, “Bi ni.”
(Ya faɗi wannan ne yana kwatanta irin mutuwar da Bitrus zai yi ya ɗaukaka Allah.) Bayan ya faɗi haka, ya ce masa, “Bi ni.”
Yesu ya ce masa, “In na nufe shi da wanzuwa har in zo, mene ne naka a ciki? Kai dai, bi ni!”
Ku kuma yā raya ku sa'ad da kuke matattu ta wurin laifofinku da zunubanku,
ko a sa'ad da muke matattu ma ta wurin laifofinmu, sai ya rayar da mu tare da Almasihu (ta wurin alheri an cece ku),
Saboda haka aka ce, “Farka, ya kai mai barci, ka tashi daga matattu. Almasihu kuwa zai haskaka ka.”
Ku kuma da kuke matattu saboda laifofinku, marasa kaciya ta jiki, Allah ya raya ku tare da Almasihu, ya yafe mana dukkan laifofinmu,
Amma wadda take zaman annashuwa kuwa, kamar matacciya take, ko da tana a raye.