Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 8:20 - Littafi Mai Tsarki

20 Yesu ya ce masa, “Yanyawa da ramummukansu, tsuntsaye kuma da sheƙunan, amma Ɗan Mutum ba shi da wurin shaƙatawa.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

20 Sai Yesu ya amsa ya ce, “Yanyawa suna da ramummuka, tsuntsayen sararin sama suna da sheƙuna, amma Ɗan Mutum ba shi da wurin da zai sa kansa.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 8:20
35 Iomraidhean Croise  

A itatuwan da suke kusa da wurin, Tsuntsaye suke yin sheƙunansu suna ta raira waƙa.


A nan tsuntsaye suke yin sheƙunansu, A bisa itatuwan fir shamuwa suke yin sheƙa.


Ni talaka ne, matalauci, Na ji zafi ƙwarai a can zuciyata.


Ba ni da ƙarfi, ba mataimaki, Ya Allah, ka zo wurina da hanzari. Kai ne mataimakina da Mai Cetona, Kada ka yi jinkiri, ya Ubangiji!


Amma ni mai bukata ne, ina shan wahala, Ka tsame ni, ya Allah, ka cece ni!


Har ba'u ma sukan yi sheƙa, Tsattsewa suna da sheƙunansu, A kusa da bagadanka suke kiwon 'ya'yansu. Ya Ubangiji Maɗaukaki, Sarkina, Allahna.


“A cikin wahayi na dare, na ga wani kamar Ɗan Mutum. Yana zuwa cikin gizagizai, Ya zo wurin wanda yake Tun Fil Azal, Aka kai shi gabansa.


Kowa ya aibata Ɗan Mutum, ā gafarta masa. Amma wanda ya aibata Ruhu Mai Tsarki, ba za a gafarta masa ba, duniya da lahira.”


Wato, kamar yadda Yunusa ya yi kwana uku dare da rana cikin wani babban kifi, haka kuma Ɗan Mutum zai yi kwana uku dare da rana a cikin ƙasa.


Domin Ɗan Mutum shi ne Ubangijin Asabar.”


Ya amsa ya ce, “Mai yafa kyakkyawan irin nan, shi ne Ɗan Mutum.


To, da Yesu ya shiga ƙasar Kaisariya Filibi, sai ya tambayi almajiransa ya ce, “Wa mutane suke cewa, Ɗan Mutum yake?”


Domin Ɗan Mutum zai zo da ɗaukakar Ubansa tare da mala'ikunsa. A sa'an nan ne zai sāka wa kowane mutum gwargwadon aikinsa.


Suna cikin gangarowa daga dutsen, sai Yesu ya kwaɓe su ya ce, “Kada ku gaya wa kowa abin da kuka gani, sai an ta da Ɗan Mutum daga matattu.”


Yesu ya ce musu, “Hakika, ina gaya muku, a sabon zamani, sa'ad da Ɗan Mutum ya zauna a maɗaukakin kursiyinsa, ku da kuka bi ni, ku ne kuma za ku zauna a kursiyi goma sha biyu, kuna hukunta kabilan nan goma sha biyu na Isra'ila.


Duk wanda zai ji kunyar shaida ni da maganata a wannan zamani na rashin amana da yawan zunubi, Ɗan Mutum ma zai ji kunyar shaida shi, sa'ad da ya zo da ɗaukakar Ubansa tare da mala'iku tsarkaka.”


“Ina kuma gaya muku, kowa ya bayyana yarda a gare ni a gaban mutane, Ɗan Mutum ma zai bayyana yarda a gare shi a gaban mala'ikun Allah.


Ina gaya muku, zai biya musu hakkinsu, da wuri kuwa. Amma kuwa sa'ad da Ɗan Mutum ya zo, zai tarar da bangaskiya a duniya ne?”


Ga alamar da za ku gani, za ku sami jariri rufe da zanen goyo, kwance a komin dabbobi.”


Sai suka tafi da hanzari, suka sami Maryamu da Yusufu, da kuma jaririn kwance a komin dabbobi.


Sai ta haifi ɗanta na fari, ta rufi shi da zanen goyo, ta kuma kwantar da shi a wani komi dabbobi, don ba su sami ɗaki a masaukin ba.


Koyaushe ku zauna a faɗake, kuna addu'a ku sami ikon tsere wa dukan waɗannan al'amura da za su auku, ku kuma tsaya a gaban Ɗan Mutum.”


da Yuwana matar Kuza, wakilin Hirudus, da Suzanatu, da kuma waɗansu da yawa da suka yi musu ɗawainiya da kayansu.


Yesu ya ce masa, “Yanyawa da ramummukansu, tsuntsaye kuma da wurin kwanansu, amma Ɗan Mutum ba shi da wurin shaƙatawa.”


Yesu kuma ya ce masa, “Lalle hakika, ina gaya muku, za ku ga sama ta dāre, mala'ikun Allah suna hawa da sauka ga Ɗan Mutum.”


Sai taron suka amsa masa suka ce, “Shari'armu ta gaya mana, cewa Almasihu zai tabbata har abada. To, yaya za ka ce lalle ne a ɗaga Ɗan Mutum? Wane ne Ɗan Mutum ɗin?”


Bayan ya fita kuma sai Yesu ya ce, “Yanzu ne aka ɗaukaka Ɗan Mutum, aka kuma ɗaukaka Allah ta wurinsa.


Ba wanda ya taɓa hawa cikin Sama sai shi wanda ya sauko daga Sama, wato, Ɗan Mutum da yake Sama.


Kamar yadda Musa ya ɗaga macijin nan a jeji, haka kuma dole ne a ɗaga Ɗan Mutum,


Kada ku yi wahala a kan neman abinci mai lalacewa, sai dai a kan abinci mai dawwama har ya zuwa rai madawwami, wanda Ɗan Mutum zai ba ku. Domin shi ne wanda Uba, wato Allah, ya tabbatar wa da ikon yin haka.”


Sai Yesu ya ce musu, “Lalle hakika, ina gaya muku, in ba ku ci naman jikin Ɗan Mutum ba, kuka kuma sha jininsa, ba rai a gare ku.


Yaya ke nan in kuka ga Ɗan Mutum yana hawa inda yake dā?


Sai ya ce, “Ga shi, ina ganin sama a buɗe, da kuma Ɗan Mutum tsaye dama ga Allah.”


Domin kun san alherin Ubangijinmu Yesu Almasihu, ko da yake shi mawadaci ne, sai ya zama matalauci sabili da ku, domin ta wurin talaucinsa ku wadata.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan