Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 8:17 - Littafi Mai Tsarki

17 Wannan kuwa domin a cika faɗar Annabi Ishaya ne cewa, “Da kansa ya ɗebe rashin lafiyarmu, ya ɗauke cucecucenmu.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

17 Wannan ya faru ne domin a cika abin da aka faɗa ta bakin annabi Ishaya cewa, “Ya ɗebi rashin lafiyarmu, ya kuma ɗauki cututtukanmu.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 8:17
9 Iomraidhean Croise  

Ibrahim ya ɗauki itacen hadayar ƙonawa, ya ɗora wa ɗansa Ishaku, shi kuma ya ɗauki wuta da wuƙa a hannunsa. Dukansu biyu kuwa suka tafi tare.


Amma ya daure da wahala wadda a ainihi tamu ce, Raɗaɗin da ya kamata mu ne za mu sha shi. Mu kuwa muna tsammani wahalarsa Hukunci ne Allah yake yi masa.


An yi wannan ne duk, don a cika abin da Ubangiji ya faɗa ta bakin annabin cewa,


ya zauna a can har mutuwar Hirudus. Wannan kuwa domin a cika abin da Ubangiji ya faɗa ne ta bakin annabin cewa, “Daga Masar na kirawo Ɗana.”


Sai ya je ya zauna a wani gari wai shi Nazarat, domin a cika faɗar annabawa cewa, “Za a kira shi Banazare.”


Da magariba, bayan faɗuwar rana, aka kakkawo masa dukan marasa lafiya, da masu aljannu.


A daidai fāɗuwar rana, duk waɗanda suke da marasa lafiya, masu cuta iri iri, suka kakkawo su wurinsa. Sai ya ɗaɗɗora wa kowannensu hannu, ya warkar da su.


Saboda haka, ina murna da raunanata, da cin mutuncin da ake yi mini, da shan wuya, da shan tsanani, da masifu saboda Almasihu, don sa'ad da nake rarrauna, a sa'an nan ne nake da ƙarfi.


Shi kansa ya ɗauke zunubanmu a jikinsa a kan gungume, domin mu yi zamanmu matattu ga zunubi, rayayyu kuma ga adalci. Da raunukansa ne aka warkar da ku.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan