Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 8:16 - Littafi Mai Tsarki

16 Da maraice ya yi, sai suka kakkawo masa masu aljannu da yawa. Da magana kawai ya fitar da aljannun, ya kuma warkar da dukan marasa lafiya.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

16 Da yamma ta yi, aka kawo masa masu aljanu da yawa, ya kuwa fitar da ruhohin ta wurin magana, ya kuma warkar da dukan marasa lafiya.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 8:16
17 Iomraidhean Croise  

Ya ce, “In za ku himmantu ku yi biyayya da ni, ni da nake Ubangiji Allahnku, sai ku aikata abin da yake daidai a gare ni, ku kuma kiyaye umarnaina da dokokina duka, to, ba zan sa muku cuce-cuce irin waɗanda na sa wa Masarawa ba, gama ni ne Ubangiji da nake warkar da ku.”


Sai aka kawo masa wani beben makaho mai aljan, ya kuwa warkar da shi, har beben ya yi magana, ya kuma gani.


Da ya fita daga jirgin ya ga babban taron mutane. Sai ya ji tausayinsu, ya kuma warkar da marasa lafiya a cikinsu.


Sai ya taɓa hannunta, zazzaɓin ya sake ta, ta kuma tashi ta yi masa hidima.


Masu kiwon aladen suka gudu, suka shiga gari, suka yi ta ba da labarin kome da kome, da kuma abin da ya auku ga masu aljannun.


Sai aka kawo masa wani shanyayye, kwance a gado. Da Yesu ya ga bangaskiyarsu, sai ya ce wa shanyayyen, “Ɗana, ka yi farin ciki, an gafarta maka zunubanka.”


Sai suka kawo masa wani shanyayye, mutum huɗu suna ɗauke da shi.


Ya faɗi haka ne domin Yesu ya ce masa, “Rabu da mutumin nan, kai wannan baƙin aljan!”


Da Yesu ya ga taro na ɗungumowa a guje, sai ya tsawata wa baƙin aljanin ya ce masa, “Kai, beben aljan, na umarce ka ka rabu da shi, kada kuma ka ƙara hawansa.”


Da Yesu ya gan ta, sai ya kira ta ya ce mata, “Uwargida, an raba ki da rashin lafiyarki!”


A daidai fāɗuwar rana, duk waɗanda suke da marasa lafiya, masu cuta iri iri, suka kakkawo su wurinsa. Sai ya ɗaɗɗora wa kowannensu hannu, ya warkar da su.


Aljannu kuma suka fita daga mutane da yawa, suna ihu suna cewa, “Kai Ɗan Allah ne!” Amma ya tsawata musu, ya hana su magana, don sun sani shi ne Almasihu.


Har ma ya kai ga suna fito da marasa lafiya tafarku, suna shimfiɗa su a kan gadaje da tabarmi, don in Bitrus ya zo wucewa, ko da inuwa tasa ma ta bi ta kan waɗansunsu.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan