Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 8:13 - Littafi Mai Tsarki

13 Sai Yesu ya ce wa jarumin, “Je ka, ya zama maka gwargwadon bangaskiyar da ka yi.” Nan take yaronsa ya warke.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

13 Sa’an nan Yesu ya ce wa jarumin, “Je ka! Za a yi bisa ga bangaskiyarka.” A daidai wannan lokaci bawansa kuwa ya warke.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 8:13
10 Iomraidhean Croise  

Yi tafiyarka, ka ci abincinka da farin ciki, ka sha ruwan inabinka da fara'a, gama abin da ka yi duka daidai ne a wurin Allah.


Sai Yesu ya amsa mata ya ce, “Kai, uwargida, bangaskiyarki da yawa take! Yă zamar miki yadda kike so.” Nan take 'ya tata ta warke.


Ya ce musu, “Saboda ƙarancin bangaskiyarku. Domin hakika ina gaya muku, da kuna da bangaskiya, ko misalin ƙwayar mustad, da za ku ce wa dutsen nan, ‘Kawu daga nan, ka koma can!’, sai kuwa ya kawu. Ba kuwa abin da zai gagare ku.


Sai Yesu ya ce masa, “Ka kula fa, kada ka gaya wa kowa kome. Sai dai ka je wurin firist ya gan ka, ka kuma yi sadaka domin tabbatarwa a gare su, kamar yadda Musa ya umarta.”


Sai Yesu ya juya, yă gan ta, ya ce, “'Yata, ki yi farin ciki, bangaskiyarki ta warkar da ke.” Nan take matar ta warke.


Sai ya ce mata, “Saboda wannan magana taki, koma gida, aljanin, ai, ya rabu da 'yarki.”


Sai Yesu ya ce masa, “In zan iya? Ai, dukkan abu mai yiwuwa ne ga mai ba da gaskiya.”


Yesu ya ce masa, “Yi tafiyarka, ɗanka a raye yake.” Mutumin kuwa ya gaskata maganar da Yesu ya faɗa masa, ya yi tafiyarsa.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan