Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 7:7 - Littafi Mai Tsarki

7 “Ku yi ta roƙo, za a ba ku. Ku yi ta nema, za ku samu. Ku yi ta ƙwanƙwasawa, za a kuwa buɗe muku.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

7 “Ku roƙa za a ba ku; ku nema za ku samu; ku ƙwanƙwasa za a kuwa buɗe muku ƙofa.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 7:7
43 Iomraidhean Croise  

Ya zama kuwa a wannan rana, barorin Ishaku suka zo suka faɗa masa zancen rijiyar da suka haƙa, suka ce masa, “Mun sami ruwa.”


Ubangiji kuwa ya bayyana ga Sulemanu cikin mafarki a Gibeyon da dare, ya ce masa, “Ka roƙi abin da kake so in ba ka.”


Za ka saurara ga addu'o'in masu kaɗaici, ya Ubangiji, Za ka ba su ƙarfin hali.


Mugun mutum da girmankansa yana cewa, “Ba Allah!” Wannan ne abin da mugu yake tunani.


Ina yabonka, Ya Ubangiji, Ka koya mini ka'idodinka!


Ka ce, “Zo wurina,” Zan kuwa zo gare ka, ya Ubangiji,


Na yi addu'a ga Ubangiji, ya kuwa amsa mini, Ya kuɓutar da ni daga dukan tsorona.


Ka nemi farin cikinka a wurin Ubangiji, Zai kuwa biya maka bukatarka.


Ku yi kira gare ni sa'ad da wahala ta zo, Zan cece ku, Ku kuwa za ku yabe ni.”


Sa'ad da masu bukata suka ga wannan za su yi murna, Waɗanda suke yi wa Allah sujada kuwa za a ƙarfafa su.


Ka sa dukan waɗanda suke zuwa gare ka Su yi murna, su yi farin ciki! Ka sa waɗanda suke ƙaunar cetonka Kullayaumi su ce, “Allah da girma yake!”


Ya Ubangiji, kai managarci ne, mai yin gafara, Cike kake da madawwamiyar ƙauna ga dukan waɗanda suke yin addu'a gare ka.


Ina ƙaunar waɗanda suke ƙaunata, Dukan wanda yake nemana kuma zai same ni.


Bari in tashi yanzu in shiga birni, In bi titi-titi, in bi dandali-dandali, In nemi wanda raina yake ƙauna. Na neme shi, amma ban same shi ba.


Ku jama'ar da suke zaune a Urushalima ba za ku ƙara yin kuka ba. Ubangiji mai juyayi ne, sa'ad da kuka yi kuka gare shi neman taimako, zai amsa muku.


“Ka kira ni, ni kuwa zan amsa maka, zan kuwa nuna maka manyan al'amura masu girma da banmamaki, waɗanda ba ka sani ba.”


Ubangiji ya ce wa jama'ar Isra'ila, “Ku zo gare ni, za ku tsira.


Har wa yau dai ina gaya muku, in mutum biyu daga cikinku, ra'ayinsu ya zo ɗaya a nan duniya a kan wani abin da za su roƙa, Ubana kuwa da yake Sama zai yi musu shi.


Kome kuka roƙa da addu'a, in dai kuna da bangaskiya, za ku samu.”


Muhimmin abu na farko, sai ku ƙwallafa rai ga al'amuran Mulkin Allah, da kuma adalcinsa, har ma za a ƙara muku dukan waɗannan abubuwa.


To, ku da kuke mugaye ma, kuka san yadda za ku ba 'ya'yanku kyautar kyawawan abubuwa, balle Ubanku na Sama da zai ba da abubuwan alheri ga masu roƙonsa?


Duk wanda ya roƙa, akan ba shi, mai nema yana tare da samu. Wanda ya ƙwanƙwasa kuma za a buɗe masa.


Don haka ina dai gaya muku, kome kuka roƙa da addu'a, ku gaskata cewa samamme ne, za ku kuwa samu.


In dai maigida ya riga ya tashi ya rufe ƙofa, kun kuma fara tsayawa daga waje, kuna ƙwanƙwasa ƙofar, kuna cewa, ‘Ya Ubangiji, buɗe mana,’ sai ya amsa muku ya ce, ‘Ku kam, ban san daga inda kuke ba.’


Ya kuma ba su wani misali cewa ya kamata kullum su yi addu'a, kada kuma su karai.


Ba ku kuka zaɓe ni ba, ni ne na zaɓe ku, na sa ku ku je ku yi 'ya'ya, 'ya'yanku kuma su tabbata, domin kome kuka roƙi Uba da sunana yă ba ku.


In kun zauna a cikina, maganata kuma ta zauna a cikinku, za ku roƙi duk abin da kuke so, za a kuwa yi muku.


Yesu ya amsa mata ya ce, “Da kin san kyautar Allah, da kuma wanda ya ce miki, ‘Sa mini ruwa in sha,’ ai, da kin roƙe shi, shi kuwa zai ba ki ruwan rai.”


Waɗanda suke neman daraja da ɗaukaka da kuma dawwama ta wurin naciyarsu ga aikata nagarta, zai saka musu da rai madawwami.


Babu wani mai fahimta, babu wani mai neman Allah.


In ba a game da bangaskiya ba kuwa, ba shi yiwuwa a faranta masa rai. Domin duk wanda zai kusaci Allah, lalle ne ya gaskata cewa, akwai shi, yana kuma sakamako ga masu nemansa.


Addu'ar bangaskiya kuwa, za ta warkar da marar lafiya Ubangiji kuma zai tashe shi, in ma ya yi zunubi, za a gafarta masa.


Mukan kuma sami duk abin da muka roƙa a gare shi, domin muna bin umarninsa, muna kuma yin abin da yake so.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan