Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 7:5 - Littafi Mai Tsarki

5 Kai munafuki! Sai ka fara cire gungumen da yake idonka tukuna, sa'an nan ka gani sosai yadda za ka cire ɗan hakin daga idon ɗan'uwanka.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

5 Kai munafuki, fara cire gungumen da yake idonka, a sa’an nan ne za ka iya gani sosai yadda za ka cire ɗan tsinken da yake a idon ɗan’uwanka.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 7:5
11 Iomraidhean Croise  

Yesu kuwa domin ya gane muguntarsu, sai ya ce musu, “Don me kuke jarraba ni? Ku munafukai!


Don me kake duban ɗan hakin da yake idon ɗan'uwanka, amma gungumen da yake a naka ido ba ka kula ba?


Ko kuwa yaya za ka iya ce wa ɗan'wanka, ‘Bari in cire maka ɗan hakin daga idonka,’ alhali kuwa da gungume a naka ido?


“Kada ku ba karnuka abin da yake tsattsarka. Kada kuma ku jefa wa alhanzir lu'ulu'unku, don kada su tattake su, su juyo su kyakketa ku.”


Munafukai! Kuna iya gane yanayin ƙasa da na sararin sama, amma me ya sa ba ku iya gane alamun zamanin ba?”


Amma Ubangiji ya amsa masa ya ce, “Munafukai! Ashe, kowannenku ba ya kwance takarkarinsa ko jakinsa a turke, ya kai shi banruwa ran Asabar?


Yesu ya ce musu, “Lalle za ku faɗa mini karin maganan nan, ‘Likita, warkar da kanka.’ Za ku kuma ce mini, ‘Duk abin da muka ji ka yi a Kafarnahum, ka yi a nan garinku mana.’ ”


Ƙaƙa kuma za ka iya ce wa ɗan'uwanka, ‘Ya ɗan'uwana, bari in cire maka ɗan hakin da yake a idonka,’ alhali kuwa kai kanka ba ka ga gungumen da yake a naka ido ba? Kai munafuki! Sai ka fara cire gungumen da yake a idonka tukuna sa'an nan ka gani sosai yadda za ka cire ɗan hakin da yake a idon ɗan'uwanka.”


Amma aljanin ya amsa musu ya ce, “Yesu dai na san shi, na kuma san Bulus, to, ku kuma ku wane ne?”


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan