Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 7:28 - Littafi Mai Tsarki

28 Da Yesu ya gama duk wannan magana, sai taro suka yi mamakin koyarwarsa,

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

28 Sa’ad da Yesu ya gama faɗin waɗannan abubuwa, sai taron mutanen suka yi mamakin koyarwarsa,

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 7:28
18 Iomraidhean Croise  

Kai ne mafi kyau a cikin dukan mutane, Kai mai kyakkyawan lafazi ne, Kullum Allah yakan sa maka albarka!


Da Yesu ya gama yi wa almajiransa sha biyun nan umarni, sai ya ci gaba daga nan domin ya koyar, yă kuma yi wa'azi a garuruwansu.


To, da Yesu ya gama duk wannan magana, sai ya bar ƙasar Galili, ya shiga ta Yahudiya, wadda take ƙetaren Kogin Urdun.


Da jama'a suka ji haka, sai suka yi mamakin koyarwarsa.


Da Yesu ya gama duk wannan magana, sai ya ce wa almajiransa,


Da ruwa ya sauko, koguna suka yi cikowa, sai iska ta taso ta bugi gidan har ya rushe, mummunar ragargajewa kuwa!”


domin yana koya musu da hakikancewa, ba kamar malamansu na Attaura ba.


Sun yi mamakin koyarwa tasa, domin yana koya musu da hakikan cewa, ba kamar malaman Attaura ba.


Da manyan firistoci da malaman Attaura suka ji wannan magana suka kuma nemi hanyar hallaka shi, saboda sun tsorata da shi, don duk jama'a na mamaki da koyarwa tasa.


Da Asabar ta yi, sai ya fara koyarwa a majami'a. Mutane da yawa da suka saurare shi, suka yi mamaki, suna cewa, “Ina mutumin nan ya sami wannan abu duka? Wace hikima ce aka ba shi haka? Dubi irin waɗannan mu'ujizan da ake aikatawa ta hannunsa!


Suka kuwa rasa abin da za su yi, saboda maganarsa ta ɗauke wa duk jama'a hankali.


Duk waɗanda suka ji shi kuwa suka yi al'ajabin irin fahimtarsa da amsoshinsa.


Duk suka yabe shi, suna mamakin maganarsa ta alheri da ya faɗa, har suka ce, “Ashe, wannan ba ɗan Yusufu ba ne?”


Suka yi mamakin koyarwarsa domin magana tasa da hakikancewa take.


Bayan da Yesu ya ƙare jawabinsa duka a gaban jama'a, ya shiga Kafarnahum.


Yahudawa suka yi mamakin abin, suka ce, “Yaya mutumin nan yake da karatu haka, ga shi kuwa, bai taɓa koyo ba?”


Sai dogaran suka amsa suka ce, “A'a, ba mutumin da ya taɓa magana kamar wannan!”


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan