Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 7:26 - Littafi Mai Tsarki

26 Kowa ya ji maganar nan tawa, bai aikata ta kuma ba, za a misalta shi da wawan mutum, wanda ya gina gidansa a kan rairayi.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

26 Amma duk wanda yake jin kalmomin nan nawa bai kuwa aikata su ba, yana kama da wani wawa wanda ya gina gidansa a kan yashi.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 7:26
9 Iomraidhean Croise  

Kafin ma su kai ga kwanakinsu, Sai rigyawa ta shafe su.


Hikimar mata takan gina gidaje, amma wauta takan rushe su.


Za a kunyatar da masu hikima. Za su tsorata, za a kuma tafi da su. Ga shi, sun ƙi maganar Ubangiji. Wace hikima suke da ita?


“Saboda haka, kowa da yake jin maganar nan tawa, yake kuma aikata ta, za a kwatanta shi da mutum mai hikima, wanda ya gina gidansa a kan fā.


Da ruwa ya sauko, koguna suka yi cikowa, iska ta taso ta bugi gidan, amma bai faɗi ba, domin an gina shi a kan fā ne.


Da ruwa ya sauko, koguna suka yi cikowa, sai iska ta taso ta bugi gidan har ya rushe, mummunar ragargajewa kuwa!”


Amma wanda ya ji maganata, bai kuwa aikata ba, kamar mutum yake wanda ya gina gida a kan turɓaya, ba harsashi. Ruwan kogi ya buge shi, nan da nan ya rushe. Wannan gida ya yi mummunar ragargajewa!”


Kai marar azanci! Wato sai an nuna maka, bangaskiya ba tare da aikatawa ba, wofiya ce?


Ni Ubangiji Allah na Isra'ila, na yi alkawari a dā cewa, ‘Kai da iyalinka da danginka za ku yi mini aikin firist har abada.’ Amma yanzu na ce ba zan yarda da wannan ba. Waɗanda suke girmama ni, zan girmama su. Waɗanda suke raina ni zan ƙasƙantar da su ƙwarai.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan