Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 7:24 - Littafi Mai Tsarki

24 “Saboda haka, kowa da yake jin maganar nan tawa, yake kuma aikata ta, za a kwatanta shi da mutum mai hikima, wanda ya gina gidansa a kan fā.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

24 “Saboda haka duk wanda yake jin kalmomin nan nawa yake kuma aikata su, yana kama da mutum mai hikima wanda ya gina gidansa a kan dutse.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 7:24
41 Iomraidhean Croise  

“Allah ya ce wa mutane, ‘Duba, tsoron Ubangiji shi ne hikima, Rabuwa da mugunta kuma, ita ce haziƙanci.’ ”


Hanyar samun hikima, ita ce tsoron Ubangiji, Yakan ba da kyakkyawar ganewa Ga dukan waɗanda suke bin umarnansa, Sai ku yabe shi har abada!


Fassarar koyarwarka takan ba da haske, Takan ba da hikima ga wanda bai ƙware ba.


Ganewata ta fi ta dukan malamaina, Saboda ina ta tunani a kan koyarwarka.


Hadiri yakan taso ya wargaza mugaye, amma amintattu lafiya lau suke a ko yaushe.


Mutane masu hankali sukan bi shawarar kirki, masu maganar wauta kuwa za su lalace.


Mugaye sukan gamu da faɗuwarsu, ba magāda, amma iyalan adalai sukan dawwama.


Me ya sa haziƙi yake da hikima? Domin ya san abin da zai yi. Me ya sa dakiki yake wauta? Domin yana ganin kansa masani ne.


Ai, kowa ya yi abin da Ubana da yake cikin Sama yake so, shi ne ɗan'uwana, shi ne 'yar'uwata, shi ne kuma tsohuwata.”


Ina dai gaya maka, kai ne Bitrus, a kan dutsen nan ne zan gina ikilisiyata, wadda ikon Hades ba zai rinjaye ta ba.


“Wane ne amintaccen bawan nan mai hikima, da ubangidansa ya ba shi riƙon gidansa, yă riƙa ba su abincinsu a kan kari?


Biyar daga cikinsu wawaye ne, biyar kuwa masu hikima.


Masu hikimar nan kuwa sun riƙo kwalaben mai da fitilunsu.


Amma masu hikimar suka amsa suka ce, ‘Ai, watakila ba zai ishe mu mu da ku ba. Gara ku je wurin masu sayarwa ku sayo.’


Da ruwa ya sauko, koguna suka yi cikowa, iska ta taso ta bugi gidan, amma bai faɗi ba, domin an gina shi a kan fā ne.


Kowa ya ji maganar nan tawa, bai aikata ta kuma ba, za a misalta shi da wawan mutum, wanda ya gina gidansa a kan rairayi.


Amma ya ce, “I, amma albarka tā fi tabbata ga waɗanda suke jin Maganar Allah, suke kuma kiyaye ta.”


In dai kun san wannan, kuna kuma aikatawa, ku masu farin ciki ne.


“In dai kuna ƙaunata, za ku bi umarnina.


In kun bi umarnina, za ku zauna cikin ƙaunar da nake muku, kamar yadda ni na bi umarnin Ubana, na kuma zauna cikin ƙaunar da yake mini.


Ku aminaina ne in kuna yin abin da na umarce ku.


Don ba ta jin shari'ar kawai mutum yake samun kuɓuta ga Allah ba, sai dai masu aikata ta, su ne za su kuɓuta.


Ta haka za mu tabbata mun san shi, in dai muna bin umarninsa.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan