Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 7:22 - Littafi Mai Tsarki

22 A ranar nan da yawa za su ce mini, ‘Ya Ubangiji, ya Ubangiji, ashe, ba mu yi annabci da sunanka ba? Ba mu fitar da aljannu da sunanka ba? Ba mu kuma yi ayyukan al'ajabi masu yawa da sunanka ba?’

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

22 Da yawa za su ce mini a wannan rana, ‘Ubangiji, Ubangiji, ashe, ba mu yi annabci a cikin sunanka ba, ba kuma a cikin sunanka ne muka fitar da aljanu, muka yi abubuwan banmamaki da yawa ba?’

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 7:22
23 Iomraidhean Croise  

Rana tana zuwa sa'ad da girmankan 'yan adam zai ƙare, zai kuma lalatar da fāriyar 'yan adam. Sa'an nan Ubangiji ne kaɗai za a ɗaukaka.


Girmankan ɗan adam zai ƙare, za a hallakar da fāriyar ɗan adam, Ubangiji ne kaɗai za a ɗaukaka sa'ad da wannan rana ta yi,


Faɗar wanda yake jin faɗar Allah, Shi wanda yake ganin wahayin Maɗaukaki, Yana durƙushe, amma idanunsa a buɗe suke.


Suka kashe har da sarakuna biyar na Madayanawa, da Ewi, da Rekem, da Zur, da Hur, da Reba. Suka kuma kashe Bal'amu ɗan Beyor.


Hakika, ina gaya muku, a Ranar Shari'a za a fi haƙurce wa ƙasar Saduma da ta Gwamrata a kan garin nan.”


“Amma fa wannan rana da wannan sa'a ba wanda ya sani, ko mala'ikun da yake Sama, ko Ɗan, sai dai Uban kaɗai.


Daga baya sai waɗancan 'yan matan ma suka iso, suka ce, ‘Ya Ubangiji, ya Ubangiji, ka buɗe mana!’


“Ba duk mai ce mini, ‘Ya Ubangiji, ya Ubangiji,’ ne zai shiga Mulkin Sama ba, sai dai wanda ya yi abin da Ubana da yake cikin Sama yake so.


Ina dai gaya muku, a ran nan, za a fi haƙurce wa Saduma a kan garin nan.”


Ba da nufinsa ya faɗi haka ba, sai dai da yake shi ne babban firist a shekaran nan, ya yi annabci cewa, Yesu zai mutu saboda jama'a,


Amma, ai, ba a cikin duhu kuke ba, 'yan'uwa, har da ranar nan za ta mamaye ku kamar ɓarawo.


wato, a lokacin da ya dawo, tsarkakansa su ɗaukaka shi, duk masu ba da gaskiya kuma su yi al'ajabinsa a ranar nan, don kun gaskata shaidar da muka yi muku.


Saboda haka, ne nake shan wuya haka. Duk da haka, ban kunyata ba, domin na san wanda na gaskata da shi, na kuma tabbata yana da iko ya kiyaye abin da na danƙa masa, har ya zuwa waccan rana.


Ubangiji ya yi masa jinƙai a waccan rana. Ka dai sani sarai yadda ya yi ɗawainiya mai yawa a Afisa.


Saura kuwa, sai sakamakon nan na aikin adalci, da aka tanadar mini, wanda Ubangiji, mahukunci mai adalci, zai ba ni a ranar nan, ba kuwa ni kaɗai ba, har da duk waɗanda suke ɗokin ganin bayyanarsa.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan