20 Don haka, da irin aikinsu za a gane su.”
20 Ta haka, ta wurin aikinsu za ku gane su.”
“Ko dai ku ce itace kyakkyawa ne, 'ya'yansa kuma kyawawa, ko kuwa ku ce itace mummuna ne, 'ya'yansa kuma munana. Don itace, da 'ya'yansa ake gane shi.
Za ku gane su ta irin aikinsu. A iya ciran inabi a jikin ƙaya, ko kuwa ɓaure a jikin sarƙaƙƙiya?
Domin kowane itace da irin 'ya'yansa ake saninsa. Ai, ba a ɗiban ɓaure a jikin ƙaya, ko kuwa inabi a jikin sarƙaƙƙiya.
To, yanzu ma, ina gaya muku, ku fita sha'anin mutanen nan, ku ƙyale su. Idan dai niyyarsu ko aikinsu na mutum ne, ai, zai rushe,
Ya 'yan'uwana, ashe, ɓaure yana iya haifar zaitun? Ko kuwa inabi ya haifi ɓaure? Haka kuma, ba dama a sami ruwan daɗi a idon ruwan zartsi.