Rassan itatuwa sun bushe sun kakkarye, mata kuwa sun tattara, don su riƙa hura wuta da su. Da yake jama'a ba su gane kome ba, Allah Mahaliccinsu ba zai ji tausayinsu ba, ba zai nuna musu jinƙai ba.
Sai ya yi magana da ƙarfi, ya ce, “ ‘A sare itacen, a daddatse rassansa, A zage ganyayensa ƙaƙaf, a warwatsar da 'ya'yansa. A sa namomin jeji su gudu daga ƙarƙashinsa, Tsuntsaye kuma su tashi daga rassansa.
Waɗannan mutane kamar aibobi ne a taronku na soyayya, suna ta shagulgulan ciye-ciye a cikinku, ba kunya ba tsoro, suna kula da kansu kawai. Su kamar holoƙon hadiri ne, wanda iska take korawa. Su kamar itatuwa ne, marasa 'ya'ya da kaka, matattu murus, tumɓukakku.