Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 7:16 - Littafi Mai Tsarki

16 Za ku gane su ta irin aikinsu. A iya ciran inabi a jikin ƙaya, ko kuwa ɓaure a jikin sarƙaƙƙiya?

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

16 Ta wurin aikinsu za ku gane su. Mutane suna iya tsinkan inabi a jikin ƙaya, ko kuwa ɓaure a jikin sarƙaƙƙiya?

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 7:16
10 Iomraidhean Croise  

Ayyukan da saurayi yake yi suke bayyana yadda yake, kana iya sani ko shi amintacce ne, mai nagarta.


“Ko dai ku ce itace kyakkyawa ne, 'ya'yansa kuma kyawawa, ko kuwa ku ce itace mummuna ne, 'ya'yansa kuma munana. Don itace, da 'ya'yansa ake gane shi.


Don haka, da irin aikinsu za a gane su.”


Albarkar Ruhu kuwa ita ce ƙauna, da farin ciki, da salama, da haƙuri, da kirki, da nagarta, da aminci,


To, amma wani zai ce, “Ai, kai kana da bangaskiya, ni kuwa sai aikatawa.” To, nuna mini bangaskiya, taka ba tare da aikatawa ba, ni kuma in nuna maka aikatawata, tabbatar bangaskiyata.


Ya 'yan'uwana, ashe, ɓaure yana iya haifar zaitun? Ko kuwa inabi ya haifi ɓaure? Haka kuma, ba dama a sami ruwan daɗi a idon ruwan zartsi.


Mutanen dā suna da karin magana cewa, ‘Daga cikin masu mugunta take fitowa.’ Hannuna dai ba zai taɓa ka ba.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan