Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 7:14 - Littafi Mai Tsarki

14 Domin kuwa ƙofar zuwa rai ƙunƙunta ce, hanyarta mai wuyar bi ce, masu samunta kuwa kaɗan ne.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

14 Amma ƙofar zuwa rai, ƙarama ce matsattsiya kuma, masu samunta kuwa kaɗan ne.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 7:14
27 Iomraidhean Croise  

Za ka nuna mini hanyar rai, Kasancewarka takan sa in cika da farin ciki, Taimakonka kuwa yana kawo jin daɗi har abada.


A kan hanyar adalci nake tafiya, Rankai a kan hanyoyin gaskiya.


Idan kuka kauce daga hanya zuwa dama ko hagu, za ku ji muryarsa a bayanku yana cewa, “Ga hanyan nan, ku bi ta.”


Za a yi babbar karauka a can, Za a kira ta, “Hanyar Tsarki.” Ba mai zunubi da zai taɓa bi ta wannan hanya, Ba wawayen da za su ruɗar da waɗanda suke tafiya can.


Ubangiji ya ce, “Ku gina, ku shirya hanya. Ku kawar da kowane abin sa tuntuɓe daga kan hanyar jama'ata!”


Haka Ubangiji ya ce, “Ku tsaya kan hanyoyi, ku duba, Ku nemi hanyoyin dā, inda hanya mai kyau take, Ku bi ta, don ku hutar da rayukanku. Amma suka ce, ‘Ai, ba za mu bi ta ba.’


Saboda haka na ƙarshe za su zama na farko, na farko kuma za su koma na ƙarshe.”


Gama da yawa ake kira, amma kaɗan ne zaɓaɓɓu.”


“Ku shiga ta ƙunƙuntar ƙofa, gama ƙofa zuwa hallaka faffaɗa ce, hanyarta mai sauƙin bi ce, masu shiga ta cikinta suna da yawa.


“Ku kula da annabawan ƙarya, waɗanda sukan zo muku da siffar tumaki, amma a zuci kyarketai ne masu ƙāwa.


Ya kira taron tare da almajiransa, ya ce musu, “Duk mai son bina, sai yă ƙi kansa, yă ɗauki gicciyensa, yă bi ni.


“Ya ku ɗan ƙaramin garke, kada ku ji tsoro, domin Ubanku na jin daɗin ba ku rabo a cikin Mulkin.


Za su fisshe ku daga jama'a. Hakika, lokaci ma na zuwa da kowa ya kashe ku, zai zaci bautar Allah yake yi.


Na faɗa muku wannan ne domin a gare ni ku sami salama. A duniya kuna shan wuya, amma dai ku yi farin ciki, ai, na yi nasara da duniya.”


suna ƙarfafa masu bi, suna yi musu gargaɗi su tsaya ga bangaskiya, suna cewa, sai da shan wuya mai yawa za mu shiga Mulkin Allah.


Kada ku biye wa zamanin nan, amma ku bar halinku ya sāke, ta wurin sabunta hankalinku ɗungum, don ku tabbatar da abin da Allah yake so, wato nufinsa kyakkyawa, abin karɓa, cikakke kuma.


Me ya sa? Don ba su neme ta ta hanyar bangaskiya ba, sai dai ta hanyar aikata aikin lada. Sai suka yi tuntuɓe da dutsen tuntuɓe,


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan