Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 7:11 - Littafi Mai Tsarki

11 To, ku da kuke mugaye ma, kuka san yadda za ku ba 'ya'yanku kyautar kyawawan abubuwa, balle Ubanku na Sama da zai ba da abubuwan alheri ga masu roƙonsa?

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

11 In ku da kuke mugaye kun san yadda za ku ba da kyautai masu kyau ga ’ya’yanku, balle Ubanku na sama, ba zai fi ku iya ba da abubuwa masu kyau, ga su waɗanda suka roƙe shi ba!

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 7:11
35 Iomraidhean Croise  

Ubangiji kuwa ya ga muguntar mutum ta ƙasaita a duniya, dukan zace-zacen tunanin zuciyarsa kuma mugunta ne kullayaumin.


Sa'ad da Ubangiji ya ji ƙanshi mai daɗi, sai ya ce, “Ba zan ƙara la'anta ƙasa sabili da mutum ba, ko da yake zace-zacen zuciyar mutum mugunta ne tun daga ƙuruciyarsa. Ba zan kuma ƙara hallaka kowane mai rai ba kamar yadda na yi a dā.


Ga shi, ka ƙara fiye da haka, ya Ubangiji Allah, gama ka yi magana, cewa, gidan bawanka zai kai kwanaki masu tsawo. Wannan ka'ida ce ta 'yan adam!


Mutum yakan sha mugunta kamar yadda yake shan ruwa, Hakika mutum ya lalace, ya zama mai rainako.


Ubangiji shi ne makiyayinmu, sarkinmu mai daraja, Yakan sa mana albarka, da alheri, da daraja, Ba ya hana kowane abu mai kyau ga waɗanda suke aikata abin da yake daidai.


Ubangiji zai arzuta mu, Ƙasarmu kuwa za ta ba da amfanin gona mai yawa.


Ya Ubangiji, kai Allah ne mai jinƙai, mai ƙauna, Mai jinkirin fushi, kullum kai mai alheri ne, mai aminci.


Ya Ubangiji, kai managarci ne, mai yin gafara, Cike kake da madawwamiyar ƙauna ga dukan waɗanda suke yin addu'a gare ka.


Saboda haka Ubangiji ya amsa ya ce, “Mace za ta iya mantawa da jaririnta, Ta kuma ƙi ƙaunar ɗan da ta haifa? Ya yiwu mace ta manta da ɗanta, To, ni ba zan taɓa mantawa da ku ba.


Zan faɗi ƙaunar Ubangiji marar ƙarewa, Zan yabe shi saboda dukan abin da ya yi mana. Ya sa wa jama'ar Isra'ila albarka mai yawa, Saboda jinƙansa da ƙaunarsa marar matuƙa.


“Zuciya ta fi kome rikici, Cuta gare ta matuƙa, Wa zai san kanta?


“Ga shi, kwanaki suna zuwa sa'ad da zan cika alkawarin da na yi wa mutanen Isra'ila da na Yahuza.


Ku komo wurin Ubangiji, ku roƙe shi, Ku ce, “Ka gafarta mana zunubanmu, Ka karɓe mu saboda alherinka, Mu kuwa za mu yabe ka da bakinmu.


Akwai wani Allah kamarka, mai yafe mugunta, Mai kawar da laifin ringin gādonsa? Ba ya riƙon fushi har abada, gama shi mai alheri ne.


Ubangiji Mai Runduna ya ce wa firistoci, “Ɗa yakan girmama mahaifinsa, bara kuwa yakan girmama maigidansa. Ni Ubanku ne, me ya sa ba ku girmama ni ba? Ni kuma Maigidanku ne, me ya sa ba ku ganin darajata? Kun raina ni, duk da haka kuna tambaya cewa, ‘Ƙaƙa muka raina ka?’


Kada ku kira kowa ‘Uba’ a duniya, domin Uba ɗaya ne yake gare ku, wanda yake cikin Sama.


Ko kuwa ya roƙe shi kifi, ya ba shi maciji?


“Saboda ƙaunar da Allah ya yi wa duniya har ya ba da makaɗaicin Ɗansa, domin duk wanda ya gaskata da shi kada ya hallaka, sai dai ya sami rai madawwami.


To, mun sani duk abin da Shari'a ta ce, ya shafi waɗanda suke ƙarƙashinta ne, don a tuƙe hanzarin kowa, duk duniya kuma tă sani ƙarƙashin hukuncin Allah take.


To, ƙaƙa? Mu Yahudawa mun fi sauran ne? A'a, ko kaɗan! Don dā ma mun ɗora wa Yahudawa da al'ummai laifi, cewa dukkansu zunubi yana iko da su.


Shi da bai hana Ɗansa ba, sai ma ya ba da shi saboda mu duka, ashe, ba zai ba mu kome tare da shi hannu sake ba?


Amma Nassi ya kulle kowa a cikin zunubi, don albarkar da aka yi alkawari saboda gaskatawa da Yesu Almasihu, a ba da ita ga masu ba da gaskiya.


Kowace kyakkyawar baiwa, da kowace cikakkiyar kyauta, daga Sama suke, sun sauko ne daga wurin Uban haskoki, wanda ba sauyawa ko wata alamar sākewa a gare shi faufau.


Ku dubi irin ƙaunar da Uba ya nuna mana, har yake ce da mu 'ya'yan Allah, haka kuwa muke. Abin da ya sa duniya ba ta san mu ba, don ba ta san shi ba ne.


Ta haka ƙauna take, wato, ba mu ne muka ƙaunaci Allah ba, sai dai shi ne ya ƙaunace mu, ya aiko Ɗansa, hadayar sulhu saboda a gafarta zunubanmu.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan