Mattiyu 6:9 - Littafi Mai Tsarki9 Saboda haka sai ku yi addu'a kamar haka, “ ‘Ya Ubanmu, wanda yake cikin Sama, A kiyaye sunanka da tsarki. Faic an caibideilSabon Rai Don Kowa 20209 “To, ga yadda ya kamata ku yi addu’a. “ ‘Ubanmu wanda yake cikin sama, a tsarkake sunanka, Faic an caibideil |
Waɗannan Lawiyawa kuma, wato Yeshuwa, da Kadmiyel, da Bani, da Hashabnaiya, da Sherebiya, da Hodiya, da Shebaniya, da Fetahiya su ne suka yi kiran sujada, suka ce, “Ku miƙe tsaye, ku yabi Ubangiji Allahnku, Ku yabe shi har abada abadin. Bari kowa ya yabi maɗaukakin sunanka, ya Ubangijii, Ko da yake ba yabon da ɗan adam zai yi har ya isa.”