Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 6:7 - Littafi Mai Tsarki

7 “In kuwa kuna addu'a, kada ku yi ta maimaitawar banza, kamar yadda al'ummai suke yi, a zatonsu za a saurare su saboda yawan maganarsu.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

7 Sa’ad da kuma kuke addu’a, kada ku yi ta maimaita magana, kamar marasa sanin Allah, domin suna tsammani za a ji su saboda yawan maganarsu.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 6:7
11 Iomraidhean Croise  

Yawan mafarkanka, da dukan ayyukanka, da yawan maganganunka duk banza ne, duk da haka ya fi maka amfani ka yi tsoron Allah.


In kuma ya ƙi sauraronsu, sai ka shaida wa ikilisiya. In kuma har ya ƙi sauraron ikilisiyar, ka maishe shi kamar bare, ko mai karɓar haraji.”


Da ya ci gaba kaɗan, sai ya fāɗi a ƙasa, ya yi addu'a ya ce, “Ya Ubana, in mai yiwuwa ne, ka ɗauke mini ƙoƙon wahalar nan. Duk da haka dai ba nufina ba, sai naka.”


Har wa yau a komawa ta biyu, sai ya je ya yi addu'a, ya ce, “Ya Ubana, in wannan ba zai wuce ba sai na sha shi, to, a aikata nufinka.”


Har wa yau ya sāke barinsu, ya koma ya yi addu'a ta uku, yana maimaita maganar dā.


Ai, al'ummai ma suna ta neman duk irin waɗannan abubuwa, Ubanku na Sama kuwa ya san kuna bukatarsu duka.


amma da suka fahimci, cewa shi Bayahude ne, suka ɗaga murya gaba ɗaya har wajen sa'a biyu, suna cewa, “Girma yā tabbata ga Artimas ta Afisawa!”


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan