Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 6:6 - Littafi Mai Tsarki

6 Amma in za ka yi addu'a, sai ka shiga lollokinka, ka rufe ƙofa, ka yi addu'a ga Ubanku wanda yake ɓoye, Ubanku kuwa da yake ganin abin da ake yi a asirce, zai sāka maka.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

6 Amma sa’ad da kake addu’a, sai ka shiga ɗakinka, ka rufe ƙofa, ka yi addu’a ga Ubanka wanda ba a gani. Ubanka kuwa mai ganin abin da ake yi a ɓoye, zai sāka maka.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 6:6
17 Iomraidhean Croise  

Sai ya shiga ya rufe ƙofa, daga shi sai yaron, ya yi addu'a ga Ubangiji.


Ubangiji yana lura da adalai, Yana kasa kunne ga koke-kokensu,


Za ka sa ya sha kunya, Ubangiji kuma zai sāka maka.


Jama'ata, ku shiga gidajenku, ku kukkulle ƙofofi, ku ɓoye kanku ɗan lokaci, kafin Allah ya huce daga fushinsa.


Zan amsa addu'o'insu tun ma kafin su gama yin addu'a gare ni.


Bayan ya sallami taron, ya hau dutse shi kaɗai domin ya yi addu'a. Har magariba ta yi yana can shi kaɗai.


don kada mutane su ga alama kana azumi, sai dai Ubanku da yake ɓoye ya gani. Ubanku kuma da yake ganin abin da ake yi a asirce, zai sāka maka.”


domin sadakarka tă zama a asirce, Ubanku kuwa da yake ganin abin da ake yi a asirce, zai sāka maka.”


Nata'ala ya ce masa, “A ina ka san ni?” Yesu ya amsa masa ya ce, “Tun kafin Filibus ya kira ka, sa'ad da kake gindin ɓaure, na gan ka.”


Yesu ya ce mata, “Kada ki riƙe ni, domin har yanzu ban hau wurin Uba ba tukuna. Sai dai ki tafi wurin 'yan'uwana ki ce musu ina hawa wurin Ubana kuma Ubanku, Allahna kuma Allahnku.”


Sai Karniliyas ya ce, “Yau kwana uku ke nan, wajen war haka, ina addu'ar ƙarfe uku na yamma a gidana, sai ga wani mutum tsaye a gabana, yana saye da tufafi masu ɗaukar ido,


Kashegari suna cikin tafiya, sun zo kusa da gari ke nan, sai Bitrus ya hau kan soro yin addu'a, wajen rana tsaka.


Amma Bitrus ya fitar da su duka waje, ya durƙusa, ya yi addu'a. Ya juya wajen gawar, ya ce, “Tabita, tashi.” Ta buɗe ido, da ta ga Bitrus, ta tashi zaune.


Masu zaman halin mutuntaka, ai, ƙwallafa ransu ga al'amuran halin mutuntaka suke yi, masu zaman Ruhu kuwa ga al'amuran Ruhu.


Saboda haka, nake durƙusawa a gaban Uban,


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan