Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 6:30 - Littafi Mai Tsarki

30 To, ga shi, Allah yana ƙawata tsire-tsiren jeji ma haka, waɗanda yau suke raye, gobe kuwa a jefa su a murhu, balle ku? Ya ku masu ƙarancin bangaskiya!

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

30 In haka Allah yake yi wa ciyawar jeji sutura, wadda yau tana nan, gobe kuwa a jefa a cikin wuta, ba zai ma fi yi muku sutura ba, ya ku masu ƙarancin bangaskiya?

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 6:30
15 Iomraidhean Croise  

Shi ne mai yiwuwa ne mugu ya yi girma kamar tsire-tsire, Masu aikata mugayen ayyuka kuma su arzuta, Duk da haka za a hallaka su ɗungum.


Nan da nan Yesu ya miƙa hannu ya kamo shi, ya ce masa, “Ya kai mai ƙarancin bangaskiya, don me ka yi shakka?”


Da Yesu ya lura da haka sai ya ce, “Ya ku masu ƙarancin bangaskiya, don me kuke magana da juna a kan ba ku zo da gurasa ba?


Sai Yesu ya amsa ya ce, “Ya ku marasa bangaskiya, kangararru na wannan zamani! Har yaushe zan zama da ku? Har yaushe kuma zan jure muku? Ku kawo mini shi nan.”


Ya ce musu, “Don me kuka firgita haka, ya ku masu ƙarancin bangaskiya?” Sa'an nan ya tashi, ya tsawata wa iskar da ruwan. Sai wurin duk ya yi tsit!


Ya ce musu, “Don me kuka firgita haka? Har yanzu ba ku da bangaskiya ne?”


Sai Yesu ya amsa musu ya ce, “Ya ku mutanen zamani marar bangaskiya! Har yaushe zan iya zama da ku? Har yaushe kuma zan iya jure muku? Ku dai kawo mini shi.”


To, ga shi Allah yana ƙawata tsire-tsiren jeji ma haka, waɗanda yau suke a raye, gobe kuwa a jefa su a murhu, balle ku? Ya ku masu ƙarancin bangaskiya!


Sai Yesu ya amsa ya ce, “Ya ku tsara marasa bangaskiya, kangararru! Har yaushe zan zama da ku, ina jure muku? Kawo ɗa naka nan.”


Sa'an nan ya ce wa Toma, “Sa yatsanka nan, ka ji hannuwana. Miƙo hannunka kuma ka sa a kwiɓina. Kada ka zama marar ba da gaskiya, sai dai mai ba da gaskiya.”


Ku kula fa, 'yan'uwa, kada wata muguwar zuciyar marar gaskatawa ta wakana ga waninku, wadda za ta bauɗar da ku daga wurin Allah Rayayye.


Domin “Duk ɗan adam kamar ciyawa yake, Duk darajarsa kamar furen ciyawa take, Ciyawar takan bushe, furen yakan kaɗe,


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan