Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 6:28 - Littafi Mai Tsarki

28 To, don me kuke damuwa a kan tufafi? Ku dubi dai furannin jeji, yadda suke girma, ba sa aikin fari, ba sa na baƙi,

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

28 “Me ya sa kuke damuwa a kan riguna? Ku dubi yadda furannin jeji suke girma mana. Ba sa aiki ko saƙa.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 6:28
13 Iomraidhean Croise  

Zan zama kamar raɓa ga Isra'ila, Isra'ila za ta yi fure kamar lili, Saiwarta za ta shiga kamar itacen al'ul.


kada kuma ku ɗauki burgami a tafiyarku, ko taguwa biyu, ko takalma, ko sanda, don ma'aikaci ya cancanci hakkinsa.


“Saboda haka ina gaya muku, kada ku damu a kan rayuwarku game da abin da za ku ci, da abin da za ku sha, ko kuwa jikinku, abin da za ku yi sutura. Ashe, rai bai fi abinci ba? Jiki kuma bai fi tufafi ba?


Wane ne a cikinku, don damuwarsa, zai iya ƙara ko da taƙi ga tsawon rayuwarsa?


Don haka kada ku damu, kuna cewa, ‘Me za mu ci’ ko? ‘Me za mu sha?’ Ko kuwa, ‘Me za mu sa?’


Amma Ubangiji ya amsa mata ya ce, “Marta, Marta! Hankalinki a tashe yake, kina kuma damuwa kan abu da yawa.


Sa'ad da suka kai ku gaban majami'u, da mahukunta da shugabanni, kada ku damu da yadda za ku mai da jawabi, ko kuwa abin da za ku faɗa,


Sai ya ce wa almajiransa, “Don haka, ina gaya muku, kada ku damu da batun rayuwarku game da abin da za ku ci, ko kuma jikinku, abin da za ku yi sutura.


Ku dubi dai furanni yadda suke girma, ba sa aikin fari, ba sa na baƙi, duk da haka, ina gaya muku, ko Sulemanu ma, shi da adonsa duk, bai taɓa yin adon da ya fi na ɗayansu ba.


Ya amsa musu ya ce, “Duk mai taguwa biyu, ya raba da marar ita, mai abinci ma haka.”


Kada ku damu da kome, sai dai a kowane hali ku sanar da Allah bukatunku, ta wurin yin addu'a da roƙo, tare da gode wa Allah.


Ku jibga masa dukan taraddadinku, domin yana kula da ku.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan